'Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar Legas daga kawo yaransa makaranta a arewa

'Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar Legas daga kawo yaransa makaranta a arewa

- Farfesa Johnson Fatokun, mataimakin shugaban jami'ar Anchor da ke Ayobo, Jihar Legas, ya gamu da sharrin 'yan bindiga

- 'Yan bindiga sanye da kakin 'yan sanda sun yi garkuwa da Farfesa Fatokun bayan ya rako 'ya'yansa makaranta a arewa

- Wata majiya ta bayyana yadda 'yan bindigar suka shiryawa Farfesa Fatokun gadar zare kafin su samu nasarar yin awon gaba da shi tare da direbansa

'Yan bindiga sun yi garkuwa da mataimakin shugaban jami'ar Anchor da ke Jihar Legas, Farfesa Johnson Fatokun.

Anchor Unviversity jami'a ce ta karatun addinin Kirista wacce sansaninta yake a yankin Ayobo a garin Legas. Darikar Yesu Zalla (Deeper Life) ne suka mallaki jami''ar.

Punch Metro ta rawaito cewa Farfesa Fatokun ya bar Legas a ranar Lahadi tare da 'ya'yansa domin dawo da su arewa, inda suke karatu.

'Yan bindiga sun kaiwa motarsa hari yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa filin tashin jiragen sama domin komawa Legas daga jihar Nasarawa.

KARANTA: Bafarawa ya bayyana dalilin da yasa Buhari yin bakin jini wurin shugabannin arewa

Majiyar Punch ta sanar da ita cewa 'yan bindigar da suka sace Farfesa Fatokun suna cikin kakin 'yan sanda.

'Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar Legas daga kawo yaransa makaranta a arewa
'Yan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar Legas daga kawo yaransa makaranta a arewa @Punch
Source: Twitter

"Da safiyar ranar Litinin ya mayar da dansa makarantar sakandire ta 'Deeper Life', sanna ya wuce jami'ar tarayya da ke Jos ya mayar da diyarsa.

"Yana kan hanyarsa ta komawa Keffi, jihar Nasarawa, daga Jos a daidai lokacin da ya yi arangama da 'yan bindigar.

KARANTA: Wautarka ta tsaya iya kanka; An gargadi gwamna Yahaya Bello akan sukar allurar rigakafin cutar korona

"Direbansa ya yi kokari, ya ki tsayawa yayin da 'yan bindigar suka kai musu farmaki. Sai dai, sun yi rashin sa'a, 'yan bindigar sun shirya musu gadar zare, sun rabu gida biyu.

"A yayin da wadancan suka biyosu suna harbin motarsu, akwai kuma wasu a gaba sun tsare hanya.

"Haka suka tarfasu, suka fito da direban Farfesa suka yi masa dukan tsiya har sai da Farfesan ya nemar masa afuwa, saboda ya ga 'yan bindigar tabbas sun harzuka. Daga nan ne suka yi gaba da su.

Punch ta rawaito cewa wakilinta ya shaida mata cewar 'yan bindigar sun fara magana da wasu shugabannin Cocin Farfesa Fatokun reshen jihar Nasarawa.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun nemi a biyasu miliyan asihirin (N20m) a matsayin kudin fansar Farfesa Fatokun.

Legit.ng ta rawaito cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta cafke Malam Ibrahim Tukur, mataimakin shugaban makarantar sakandire a karamar hukumar Rimi bisa zarginsa da yi wa daya daga cikin dalibansa ciki.

An kama Malam Ibrahim ne bayan dalibar da ya yi wa ciki, mai shekaru goma sha biyu, ta haihu, amma ta hanyar yi mata tiyatar ciro jariri.

A ranar Laraba ne rundunar 'yan sanda ta yi holin masu kaifuka daban-daban, cikinsu har da Malam Ibrahim.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel