Da duminsa: Buhari ya sake nada Hadiza Bala-Usman matsayin shugabar NPA

Da duminsa: Buhari ya sake nada Hadiza Bala-Usman matsayin shugabar NPA

- Bayan karewar wa'adinta na farko, Buhari ya baiwa Hadiza Bala dama ta biyu

- Hadiza Bala-Usman ta kasance ta kusa da gwamna El-Rufa'i kafin nada ta shugabar NPA a 2016

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da sake nada Hadiza Bala-Usman a matsayi Dirakta Manajan hukumar tashar ruwan Najeriya NPA, na tsawon wasu shekaru biyar.

Hakan na kunshe cikin jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya saki ranar Alhamis, a Abuja.

Jawabin ya kara da cewa Buhari ya amince da sauye-sauyen kwamitin shugabannin NPA da kuma Emmanuel Olajide Adesoye matsayin shugaba.

Sauran mambobin kwamitin amintattun sune; Prince Ekenyem Nwafor-Orizu (Yankin Kudu maso gabas), Akinwunmi Ricketts (Yankin Kudu maso kudu), Ghazali Mohammed Mijinyawa (Yankin Arewa maso gabas), Mustapha Amin Dutse (Yankin Arewa maso yamma), da Abdulwahab Adesina (Yankin Arewa maso tsakiya).

Hakazalika shugaba Buhari ya amince da nadin mambobin kwamitin amintattun kamfanin raba wutar lantarkin Najeriya (TCN), wadanda zasu zabi sabon shugaban hukumar.

Sune; Muhammad K. Ahmad, OON, (Chairman), Chief Henry Okolo, Imamudden Talba, Ambassador Usman Sarki, Ali Haruna, Engr Simeone Atakulu, Zubaida Mahey Rasheed, Dr Mustapha Abiodun Akinkunmi, Engr Oladele Amoda, and Dr Nkiru Balonwu.

Sauran mambobin kwamitin sune; wakilin ma'aikatar kudi, wakilin ma'aikatar ma'aikatar saye-saye, wakilin kamfanin wuta, da kuma wakilin TCN.

DUBA NAN: Uwargidar Zakzaky, Hajiya Zeenatu, ta kamu da Coronavirus

Da duminsa: Buhari ya sake nada Hadiza Bala-Usman matsayin shugabar NPA
Da duminsa: Buhari ya sake nada Hadiza Bala-Usman matsayin shugabar NPA
Source: Instagram

KU KARANTA: Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da aka yiwa masu batanci ga Annabi 2 a Kano

A bangare guda, Gwamnatin tarayya ta ce sahun farko na magungunan cutar COVID-19 da kamfanin Pfizer suka hada zai shigo Najeriya zuwa karshen Junairun bana.

Jaridar Daily Trust ta rahoto shugaban hukumar kiwon lafiya na NPHCDA, Dr. Faisal Shuaib, ya na wannan jawabi a ranar Talata, 19 ga watan Junairu, 2021.

Faisal Shuaib ya bayyana haka ne yayin da 'yan jarida suka ziyarci wasu dakuna na musamman da aka yi tanadi domin ajiye wadannan magunguna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel