Buhari ya jagoranci taron FEC na farko a 2021, ya rantsar da sabbin kwamishinoni hudu
- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya halarci yaron majalisar zartarwa (FEC) na farko a cikin sabuwar shekarar 2021
- Wannan shine karo na 30 da gwamnatin tarayya ta gudanar da taron FEC ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo
- Yayin taron, shugaba Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni biyu a hukmar CCB da PSC
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya halarci taron majalisar zartarwa ta tarayya na farko a cikin shekarar 2021.
Taron, wanda shine karo na 30 da aka yi ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo, ya samu halartar wasu manyan jami'an gwamnati a zahiri da suka hada da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Obasanjo, da sakataren gwamnatin tarayya; Boss Mustapha.
Akwai shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, da ministoci guda tara da suka hada da ministan shari'a, Abubakar Malami, takwaransa na sufuri, Rotimi Amaechi, da Muhammadu Dingyadi, ministan harkokin 'yan sanda.
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan, tare da sauran ministoci suna halartar taron ta kafar yanar gizo daga ofisoshinsu, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
KARANTA: CBN ta bawa gwamnatin jihar Kano tallafin biliyan goma
KARANTA: Rundunar 'yan sanda: Mun gano silar mutuwar budurwa a gidan saukar baki na gwamnatin Yobe
Sauran ministocin da suka halarci taron a zahiri sune kamar haka; Ministan, Adamu Adamu, na kasuwanci da saka hannun jari, Niyi Adebayo, ministan muhalli, Muhammad Mahmood, da na noma da raya karkara, Sabo Nanono.
Jim kadan kafin fara taron, shugaba Buhari ya rantsar da wasu sabbin kwamishinoni guda uku a hukumar da'ar ma'aikata (CCB) da kuma sabon kwashina guda daya a hukumar kula da rundunar 'yan sanda (PSC).
Legit.ng ta rawaito cewa tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, ya ce zasu ƙirƙiro sabuwar tafiyar siyasa nan bada jimawa ba.
Okorocha ya bayyana hakan ne a ranar litinin, 18 ga watan Junairu 2021.
Tsohon gwamnan na jihar Imo a karkashin jam'iyyar APC ya ce PDP da APC sun kada ƴan Najeriya ƙasa wanwar
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng