CBN ta bawa gwamnatin jihar Kano tallafin biliyan goma

CBN ta bawa gwamnatin jihar Kano tallafin biliyan goma

- Gwamnatin jihar Kano ta samu tallafin biliyan goma daga babban bankin kasa (CBN)

- A cewar Hajiya Hama Ali, darektar KanInvest, ta ce za'a yi amfani da kudaden domin tallafawa kamfanoni

- Hajiya Hama ta ce kamfanoni da yawa a jihar Kano sun shiga mawuyacin hali sakamakon bullar annobar korona

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa ta samu tallafin zunzurutun kudi har biliyan goma daga babban bankin kasa (CBN) domin farfado da masana'antun da suka jigata saboda bullar annobar korona.

Hajiya Hama Ali, babbar darekta a hukumar bunkasa harkokin saka jari a jihar (KanInvest), ita ce ta sanar da hakan yayin wani taro a Kano, kamar yadda BBC ta rawaito.

A cewarta, farfado da masana'antun zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin jihar Kano.

Akwai kimanin kamfanoni hamsin da zasu samu tallafi daga cikin kudaden domin su samu damar murmurewa daga durkushewa saboda daina aiki saboda barkewar annobar korona.

KARANTA: Tsofaffin gwamnoni na shirin ƙirƙirar sabuwar babbar jam'iyyar haɗaka

Hajiya Hama ta bayyana cewa zasu zauna da kamfanonin daya bayan daya domin jin ta bakinsu akan irin tallafin da kowanne kamfani ke bukata.

CBN ta bawa gwamnatin jihar Kano tallafin biliyan goma
CBN ta bawa gwamnatin jihar Kano tallafin biliyan goma @APC Kano
Asali: Facebook

Ta ce har yanzu kofa a bude take domin karbar fom din nuna sha'awar neman tallafi ga kamfanoni.

Kazalika, ta sanar da cewa CBN ya bada tabbacin kara yawan adadin kudin idan da bukatar hakan.

KARANTA: Kaduna: Jami'an tsaro sun kai wa 'yan bindiga harin kwanton bauna, sun kashe bakwai

Babbar darektar ta ce za'a rufe karbar fom din da aka cike a ranar 25 ga watan Fabarairu, 2021.

Legit.ng ta rawaito cewa wata kungiya mai lakabin UGPRO ta sake shigar da karar Yakubu Dogara a gaban kotun tarayya da ke Abuja

A ranar Litinin ne kotun ta saurari karar da jam'iyyar PDP ta shigar da Dogara tare da bayyana cewa yanzu ba mamba bane a cikinta.

Dukkan masu karar na neman kotun ta tsige Dogara saboda ya samu nasara ne a karkashin inuwar jam'iyyarsu.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng