Korona ta hallaka biloniya Aare Boluwatife, daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria

Korona ta hallaka biloniya Aare Boluwatife, daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria

- Biloniya, hamshakin dan kasuwa, Aare Boluwatife, ya rasu ranar Laraba bayan kamuwa da kwayar cutar koron

- Marigayi Aare, dan asalin masarautar Owu a jihar Ogun, yana daga cikin attajiran duniya da suka mallaki motocin alfarma na Rolls Royce masu yawa

- Harkokin kasuwancinsa sun hada da harkar fetur da gas, dillancin kasa da gine-gine, banki da sauransu

Cutar korona ta yi sanadiyyar rasuwar biloniya kuma hamshakin dan kasuwa, Aare Boluwatife Akin-Olugbade, a ranar Laraba.

Lindaikejiblog ta wallafa cewa dan kasuwar ya rasu sakamakon kamuwa da kwayar cutar korona.

Marigayin, dan asalin masarautar Owu a jihar Ogun, yana daga cikin attajiran duniya da suka mallaki motocin alfarma na kamfanin Rolls Royce masu yawan bada labari.

Kaunarsa da motocin kamfanin yasa shi sayen samfuri daban-daban har guda goma wadanda ya makalawa lambobi 'BOLU 1, 2, 3, har zuwa 10.

KARANTA: Rundunar 'yan sanda ta karrama marigayi AIG Bishi da faretin bankwana, an binne gawarsa cikin hawaye

Ya rasu yana da shekaru 64 a duniya.

Korona ta hallaka biloniya Aare Boluwatife, daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria
Korona ta hallaka biloniya Aare Boluwatife, daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria @Lindaikejiblog
Asali: Twitter

Marigayi Akin-Olugbade ya halarci makarantar Corona da ke Yaba, King's College da Jami'ar London inda ya karanta shari'a.

KARANTA: Fasto Yuana: Shekau yana cikin halin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria

Ya yi karatun digiri na biyu a jami'ar California (Amurka) kafin daga bisani ya yi karatun digiri na uku a jami'ar Cambridge.

Harkokin kasuwancinsa sun hada da harkar fetur da gas, dillancin kasa da gine-gine, banki da sauransu.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da uwargidansa, Aisha Buhari, sun yi alhini tare da juyayin mutuwar wata mai kusanci da su, Hajiya Nafisatu Galadima Aminu Usman.

Marigayiya Nafisatu mata ce wurin Laftanar Kanal IG Usman, dogarin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari.

A cikin sakon da kakakinsa, Garba Shehu, ya fitar ranar Talata, Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga gidan sarautar Adamawa, gwamnatin jiha da kuma jama'ar jihar baki daya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel