Kano: An gano dalilin da yasa kananan yara ke zama 'yan sholisho, an ji ta bakinsu

Kano: An gano dalilin da yasa kananan yara ke zama 'yan sholisho, an ji ta bakinsu

- Jihar Kano ta yi kaurin suna wajen matsalar yawan sha da sayar da kayan maye kala-kala

- Matsalar zukar sinadarin 'Sholisho' na kara kunna kai a tsakani yara masu tasowa a birnin Kano

- Hukumomin sun fi mayar da hankali wajen yaki da kayan maye a tsakanin matasa

Jihar Kano ta yi kaurin suna wajen matsalar yawaitar matasa da ke amfani da kayan maye daban-daban.

A cikin shekarar 2019, hukumomi sun bayyana Kano a matsayin jiha ta uku da ake da yawan masu shaye-shaye a Nigeria da adadin fiye da kaso 70% na matasa da ke amfani da kayan maye.

Jaridar HumAngle ta wallafa rahoto na musamman akan matsalar shan Sholisho a tsakanin kananan yara masu tasowa.

HumAngle ta rawaito cewa hukumar yaki da sha da hana safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta fi mayar da hankali wajen yaki da kayen maye a tsakanin matasa.

Watakila, karancin ma'aikata da kayan aiki ne yasa Jami'an hukumar NDLEA suka fi mayar da hankali akan da matasa da sauran kayan maye.

KARANTA: Bauchi: Ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu ya faskara bayan gobara ta tashi a gidansu

Binciken HumAngle ya gano cewa mafi yawa daga cikin yaran da ke Shan Sholisho almajirai ne da kuma 'ya'yan talakawa, marasa galihu.

Kano: An gano dalilin da yasa kananan yara ke zama 'yan sholisho, an ji ta bakinsu
Kano: An gano dalilin da yasa kananan yara ke zama 'yan sholisho, an ji ta bakinsu @HumAngle
Source: Twitter

Yawancin 'yan Sholisho da HumAngle ta gani a kasuwar Kurmi da ke birnin Kano almajirai ne da suka koyi shan sinadarin daga wurin wasu almajiran da ke gaba da su.

Saleh Inusa, wani yaro ne mai shekaru 14 da ya fara shan Sholisho tun bai fi shekara 10 ba.

KARANTA: Korona ta hallaka daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria, ya rasu ya bar Rolls Roys 10

A cewar Saleh, yana shan Sholisho ne saboda ya fi dukkan sauran kayan maye araha da saukin samu.

Wani matashi, Abdullahi Danladi, mai shekaru 25, ya ce bada son ransu suke shan Sholisho ba, kaddara ce da mutum bai isa ya tsallake ba, a cewarsa, yana mai kafa hujja da fadar Annabi Muhammad.

Wasu daga cikin masu Shan Sholisho sun alakanta hakan da tasirin abokai da kuma gazawar iyaye daga gidajen da suka fito.

Sholisho wani sinadari ne da masu like tayar Babur da Keke amfani da shi wajen aikinsu na 'Faci'.

Mashaya Sholisho basu da ilimi, a saboda haka basu damu da rubutun da aka yi a jikinsa akan cewa yana da matukar hatsari ga lafiya.

Saboda sukurkuta musu kwakwalwa da Sholisho ke yi da kuma ganinsu da ake yi a matsayin mahaukata, jami'an tsaro basu damu da kama masu shan sinadarin ba, ko an kamasu basa dadewa ake sakinsu.

Legit.ng ta rawaito cewa Cif Doyin Okupe, kakakin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya wallafa wata makala akan rashin tasirin kwayar cutar korona a tsakanin talakawa mazauna nahiyar Afrika.

Okupe ya yi ikirarin cewa yana da kwafin rahoton wani bincike Wanda masana kimiyya suka gudanar.

A cewar Okupe, rahoton ya bayyana cewa masana kimiyya sun alakanta karfin garkuwar jikin mutane da sinadarin vitamin D3 wanda ake samu daga hasken rana.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel