Bauchi: Jama'a sun gaza ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu bayan gobara ta tashi a gidansu

Bauchi: Jama'a sun gaza ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu bayan gobara ta tashi a gidansu

- Wata uwa da 'ya'yanta guda biyu sun rasa rayukansu a cikin yanayi mai cike da ban tausayi bayan tashin gobara a gidansu

- Uwar da 'ya'yanta gida biyu sun rasa ransu duk da ihun da neman taimakon da suka dinga yi bayan tashin gobarar

- Wani shaidar gani da ido ya ce ceton uwar da yaranta ya faskara saboda an gaza balle kofar gidansu

Wata wutar gobara da ta tashi a kauyen Riban Garmu da ke mazabar Dewu, karama hukumar Kirfi, jihar Bauchi, ta yi sanadin mutuwar wata mata da 'ya'yanta guda biyu.

Kazalika, karin wasu mutane hudu sun samu raunuka sakamakon tashin gobarar a ranar Alhamis, kamar yadda The Nation ta rawaito.

The Nation ta rawaito cewa gobarar ta tashi ne sakamakon haduwar wayoyin wutar lantarki a gidan da iyalin ke zaune.

Gidan da aka yi gobarar ya kone kurmus, kazalika an garzaya da mutane hudu da suka samu rauni zuwa asibiti.

KARANTA: Korona ta hallaka daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria, ya rasu ya bar Rolls Roys 10

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa duk da ihun neman taimako da mamatan suka dinga yi, an gaza balle kofar shiga gidan domin cetonsu.

Bauchi: Jama'a sun gaza ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu bayan gobara ta tashi a gidansu
Bauchi: Jama'a sun gaza ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu bayan gobara ta tashi a gidansu
Source: UGC

Mamba mai wakiltar karamar hukumar Kirfi a majalisar dokokin jihar Bauchi, Abdulkadir Umar Dewu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

KARANTA: Rahama Sadau na fuskantar sabuwar caccaka sakamakon hoton da ta sake saki a yanar gizo

Honarabul Dewu ya ziyarci dangin mamatan domin jajanta musu da yi musu ta'aziyya.

Kazalika, ya basu gudunmar N250,000 amadadin gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

A ranar Litinin, 11 ga watan Janairu, Legit.ng ta rawaito cewa Jarumar Kannywood, Rahama sadau, na fuskantar sabuwar caccaka daga masoyanta Musulumai sakamakon bayyana bangaren jikinta

Mabiyan jarumar sun mayar mata da martani kan hoton da ta ɗauka da jarumar masana'antar Bollywood, Shabnam Surayyo

Sai dai jarumar ta dawo shafinta na Tuwita ta wallafa wata maganar da Priyanka Chopra ta taba yi akan jajiracewa yayin suka da tsangwama.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel