Babu jihar da za'a samu zaman lafiya idan ba'a samu a Borno ba; Zulum ya fadi dalili

Babu jihar da za'a samu zaman lafiya idan ba'a samu a Borno ba; Zulum ya fadi dalili

- Har yanzu gwamnatin tarayya na cigaba da yaki da mayakan kungiyar Boko Haram musamman a jihar Borno

- Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce sai an samu zaman lafiya a jiharsa kafin sauran sassan Nigeria su zauna kalau

- Zulum ya bayar da misalai da wasu kasashen duniya da ke fama da matsalolin rashin tsaro

Babagana Zulum, gwamnan Borno, ya ce idan har jihar ba ta kasance cikin lumana ba, sauran sassan kasar ba za su taba zama cikin lumana ba, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Sama da shekaru goma, Borno da wasu jihohin arewa maso gabas na fama da hare-hare daga maharan Boko Haram, inda aka kashe dubbai tare da raba mutane sama da miliyan biyu da muhallansu.

A lokacin da yake jawabi a wajen taron lakcar shekara ta Gani Fawehinmi karo na 17 a Legas, Zulum ya ce kalubalen tsaro a Borno na da hadari ga kowane bangare na kasar kuma dole ne kowa ya taru ya a yaki hakan.

Ni daga jihar Barno nake, kuma da yawa daga cikin yaranmu suna cikin kungiyar Boko Haram. Ba na musun gaskiyar.

KARANTA: An gano dalilin da yasa kwayar cutar korona ta gaza yin tasiri a tsakanin talakawan Nigeria

"Amma kuma, mutane da yawa suna ɗaukar nauyinsu a duk faɗin duniya. A cikin kungiyar ta Boko Haram, muna da fararen fata, 'yan yankin Asiya, ‘yan Afirka, Musulmi da Kirista,” in ji shi.

Babu jihar da za'a samu zaman lafiya idan ba'a samu a Borno ba; Zulum ya fadi dalili
Babu jihar da za'a samu zaman lafiya idan ba'a samu a Borno ba; Zulum ya fadi dalili
Asali: UGC

A duk arewacin Najeriya, musamman jihar Borno, an kafa wani kwamiti domin aiki akan yadda za a sake fasalin tsarin karatun Almajiri.

"Muna so mu inganta tsarin ilimin boko da na zamani don wadatar da wadannan yara ilimin boko da na lissafi domin su iya tsayawa da kansu. Kuma ba ma goyon bayan barace-barace a kan titi.

KARANTA: Tsohon kwamishinan Ganduje: Duk da ilimin gwamna, wasu tantirai kuma jahilai ke sarrafa akalar gwamnatin Kano

“Dole ne mu daina ganin wannan fitinar a matsayin matsalar arewa. Nisan da ke tsakanin jihar Borno da jihar Legas ya kai kimanin kilomita 1,700, amma fa a kula idan har jihar Borno ba ta kasance cikin lumana ba, sauran bangarorin kasar nan ba za su taba samun zaman lafiya ba.

"Dole ne mu hada kai mu yaki wadannan mahara. Mun ga abin da ya faru a Libya, Iraki da sauran ƙasashe. Gina zaman lafiya da haɗin kan jama'a suna da matukar mahimmanci wajen ƙara ƙarfin al'ummominmu.

“Matukar bamu kawar da son zuciya, kabilanci da kuma amfani da addini ba, ba za mu taba ganin daidai a kasar nan ba.

"Tsarin mulki ya bayyana karara kan bukatar zaman lafiya a tsakaninmu baki daya, shi yasa ma aka sanya tsarin dabi'ar tarayya a cikin kundin tsarin mulki, amma shi kansa kundin tsarin mulkin an ci zarafinsa. "

Duk da an yi ta kiraye-kirayen a kirkiro ‘yan sandan jihohi don su taimaka game da tsaron cikin gida, amma gwamnan ya ce ba ya goyon bayan wannan ra’ayin, yana mai cewa hakan zai kara kawo rudani ga tsarin da ya rigaya ya lalace kuma zai raunana hadin kan kasa.

Saboda hadin kan kasa, ba zan ba da shawarar a kirkiro‘ yan sandan jihohi ba. Lokaci bai yi ba da za'a iya hakan, amma idan lokaci ya yi, ra'ayin samun 'yan sandan jihohi yana da kyau sosai. Na cancanci ra’ayina, ”in ji shi.

A wani labarin, Legit.ng Hausa rawaito cewa Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram, ƙasashen Yamma sun fi nuna damuwa da jihar Borno sama da ƙasashen Larabawa waɗanda suma suke fama da irin wannan matsalar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin ambasadan Falasɗinawa, Saleh Fheised Saleh, inda ya jinjinawa yankin na Falasɗinu da zama ɗaya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya.

A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta bawa Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel