Korona: NYSC ta hana taron ibada, ta daga ranar bude sansanin horo
- Hukumar NYSC ta ce ta dakatar da taron ibada bayan an bude sansanin bawa matasa horo a cikin watan nan
- NYSC ta ce ba zata yi sanya ba wajen korr duk wani matashi da aka samu da laifin sabawa matakan kare kai daga kamuwa da korona
- Kazalika, NYSC ta yi gargadin cewa duk matashn da ya yi jinkirin zuwa sansanin horo akan lokaci zai iya rasa gurbinsa a wannan zagayen
Hukumar kula da matasa masu hidimar kasa (NYSC) ta sanar da hana taron ibada a dukkan sansaninta da ke jihohin Nigeria.
Dakta Oyeladun Okunromade, darektan da ke jagorantar bude sansanin bayar da horo na NYSC, shine ya sanar da hakan ranar Juma'a yayin wani taro, kamar yadda The Nation ta rawaito.
An yi taron domin tattaunawa a matakan da za'a dauka yayin da aka bude sansanin bayar da horo domin karbar matasa a jimka ta II a rukunin B na shekarar 2020.
Taron, wanda aka yi a yanar gizo, ya samu halartar shugaban hukumar NYSC, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, da shugaban cibiyar dakile cututtuka masu yaduwa a Nigeria (NCDC), Dakta Chikwe Ihekweazu.
KARANTA: Korona ta hallaka daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria, ya mutu ya bar Rolls Royce 10
Ibrahim ya bayyana cewa yanzu za'a bude sansanin bayar da horo a dukkan jihohi daga ranar 19 ga watan Janairu sabanin ranar 18 da aka sanar a baya.
A cewar Birgediya Janar Ibrahim, NYSC ba zata bata lokaci wajen korar duk wani matashi da aka samu yana saba matakan da aka gindaya ba.
KARANTA: Bauchi: Ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu ya faskara bayan gobara ta tashi a gidansu
A jawabinsa, Okunromade ya ce za'a gwada kowanne matashi kafin ya shiga sansanin bayar da horo.
Ya kara da cewa za'a killace duk wanda aka samu dauke da kwayar cutar a cibiyar killacewa mafi kusa.
NYSC ta yi gargadin cewa dukkan matashin da bai bayyana a sansanin bayar da horo akan lokaci ba yana cikin hatsarin rasa gurbinsa a wannan zagayen, sai dai ya jira na gaba.
A rnar Alhamis ne Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sabunta sharudan da makarantu zasu cika da matakan da zasu dauka bayan sun bude a ranar 18 ga watan Janairu.
Ministan ilimi, Adamu Adamu, a ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu, ya sanar da cewa za'a bude makarantu kamar yadda aka tsara.
Ana shawartar Malamai su tabbatar dalibai sun nesanta da juna a ajuzuwansu tare da tilasta biyayya ga dukkan matakan kare kai.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng