Ba ziyara, ba taron "assembly"; FG ta sabunta sharuda bayan bude makarantu

Ba ziyara, ba taron "assembly"; FG ta sabunta sharuda bayan bude makarantu

- Gwamnatin tarayya ta sabunta sharudan da makarantu zasu dauka bayan sun bude a ranar 18 ga watan Janairu

- A ranar Alhamis, 14 ga watan Janairu, ministan ilimi, Adamu Adamu, ya sanar da cewa za'a bude makarantu kamar yadda aka tsara

- Ana shawartar Malamai su tabbatar dalibai sun nesanta da juna a ajuzuwansu tare da tilasta biyayya ga dukkan matakan kare kai

Biyo bayan amincewa da bude makarantu ranar 18 ga watan Janairu, gwamnatin tarayya ta sabunta sharudan da kowacce makaranta za ta dauka bayan an koma.

Jaridar Punch ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da ziyara da taron fadakar da dalibai Wanda aka fi sani da "Assembly".

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwar mai dauke da sa hannun Ben Bem Goong, darektan yada labarai a ma'aikatar ilimi.

A takardar, Ben ya jaddada cewa Ministan ma'aikatar ilimi, Adamu Adamu, ya amince a bude makarantu ranar 18 ga wata kamar yadda aka tsara.

KARANTA: Faifan bidiyon sabuwar wakar Hausa ya fusata Hausawa, sun yi tofin Ala-tsine

Ya kara da cewa; biyo bayan hakan ne aka sabunta sharudan da makarantu zasu bi tare da matakan da zasu dauka.

Ba ziyara, ba taron "assembly"; FG ta sabunta sharuda bayan bude makarantu
Ba ziyara, ba taron "assembly"; FG ta sabunta sharuda bayan bude makarantu
Asali: UGC

An bukaci makarantu su tanadi wuraren killace wadanda aka samu dauke da kwayar cutar tare da samar da wurin gwaji.

KARANTA: Bauchi: Ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu ya faskara bayan gobara ta tashi a gidansu

Kazalika, an tsawatar da makarantu akan tsaftar muhalli da kuma tabbatar da lalata bola ta hanyoyin da suka dace.

An ratayawa Malamai da sauran ma'aikata a makarantu alhakin tabbatar da yin biyayya ga dukkan sharudan da aka zayyana.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa al'ummar Hausawa ma'abota amfani da dandalin sada zumunta sun yi Alla-wadai da tofin Ala-tsine akan sakin wani faifan sabuwar wakar Hausa.

Wani mawaki ne mai suna Abdullahi Aliyu Shelleng, haifaffen jihar Adamawa, ya rewa wakar mai suna 'North Vibe'.

Wasu daga cikin masu sukar wakar sun nemi a goge faifan bidiyon daga yanar gizo sannan dauki hukuma ta dauki mataki.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng