Hotuna: Hadiman Buhari uku daga Kano sun kaiwa Kwankwaso ziyarar ta'aziyya

Hotuna: Hadiman Buhari uku daga Kano sun kaiwa Kwankwaso ziyarar ta'aziyya

- Wasu hadum miman shugaban kasa, Muhammadu Buhari, gud uku sun kaiwa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso, ziyara

- Hadiman guda uku; Bashir Ahmad, Nasiru Adahama, da Gambo Manzo, sun ziyarci Kwankwaso domin yi masa ta'aziyyar rashin mahaifinsa

- A ranar 24 ga watan Dismba ne Allah ya yiwa mahaifin Kwankwaso, Musa Saleh, rasuwa a Kano

Wasu hadiman shugaban kasa, Muhamadu Buhari, guda uku sun ziyarci tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, domin yi masa ta'aziyyar rauwar mahaifinsa.

A ranar 25 ga watan Disamba ne Allah ya yi wa majidadi, hakimin Madobi, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso, rasuwa a Kano.

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Bashir Ahmad, ya ce shi da sauran abokan aikinsa; Nasiru Sa'idu Adahama, da Gambo Manzo, sun ziyarci Kwankwso domin yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa.

Kazalika, Isma'il Ahmed, wani hadimin shugaban kasa, ya ziyarci Kwankwaso ranar Laraba domin yi masa ta'aziyya.

KARANTA: Korona ta hallaka daya daga cikin manyan 'yan kasuwa a Nigeria, ya mutu ya bar Rolls Royce 10

Marigayi Musa Saleh shine mahaifi wurin tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon sanatan Kano ta tsakiya, Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya.

Sakatare na musamman ga tsohon gwamna Kwankwaso, Mohammed Inuwa, ya sanar da rasuwar basaraken a daren ranar 24 ga watan Disamba, 2020, sakamakon takaitacciyar rashin lafiyar da ya yi a Kano.

KARANTA: Ceton wata uwa da 'ya'yanta biyu ya faskara bayan gobara ta tashi a gidansu

Inuwa ya bayyana cewa; "marigayi Alhaji Musa Saleh Kwankwaso shine mahaifin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano. Ya rasu ya bar mata biyu, 'ya'ya 19 (maza tara, mata 10) da jikoki da dama.

Al'ummar Hausawa ma'abota amfani da dandalin sada zumunta sun yi Alla-wadai da tofin Ala-tsine akan sakin wani faifan sabuwar wakar Hausa.

Wani mawaki ne mai suna Abdullahi Aliyu Shelleng, haifaffen jihar Adamawa, ya rewa wakar mai suna 'North Vibe'.

Wasu daga cikin masu sukar wakar sun nemi a goge faifan bidiyon daga yanar gizo sannan dauki hukuma ta dauki mataki.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel