Kotu ta yankewa Fasto shekaru 140 a Kurkuku kan laifin lalata yaran cikinsa

Kotu ta yankewa Fasto shekaru 140 a Kurkuku kan laifin lalata yaran cikinsa

- An damke Faston da ya bata yara haihuwan cikinsa biyu a kasar Kenya

- Dukkan wadannan yara yan makarantun firamare ne

- Alkalin ya yanke masa hukuncin dauri a gidan kaso na lokaci mai tsawon gaske

Wata kotun Baricho dake Kirinyaga Kenya ta yanke wa wani Fasto da ya lalata yaransa mata biyu kuma yayi musu juna biyu hukuncin daurin shekaru 140 a gidan kaso.

Faston dan shekara 51 mai suna John Gichini ya gurfana gaban kotun Majistaren ne ranar alhamis kuma Alkali Anthony Mwicigi ya yanke masa hukuncin shekaru 70 kan kowace yarinya.

Amma Alkalin ya ce zai ci zaman shekarun a lokaci guda.

Yayinda ake karanto masa laifukansa, an gano cewa ya aikata lalatan ne da yarinyarsa ta farko mai shekaru 16 da haihuwa a watan Yunin 2020, a kauyen Kinyakiru, kuma yanzu tana da cikin watanni 7.

Laifinsa na biyu shine lalata yarinyarsa yar shekara 14 wacce ya zakkewa a watan Agusta 2020 kuma yanzu tana dauke da cikin wata shida.

Dukkan yaran yan makarantun firamare.

Bayan aikata lalatan, Faston ya gudu daga gari amma aka damkeshi a makon farko na watan Junairu.

KU KARANTA: Sai bayan awanni 3 da muka kira yan sanda suka zo, shugaban APC da aka sacewa yara 7

Kotu ta yankewa Fasto shekaru 140 a Kurkuku kan laifin lalata yaran cikinsa
Kotu ta yankewa Fasto shekaru 140 a Kurkuku kan laifin lalata yaran cikinsa Hoto: TVC News
Asali: UGC

KU DUBA: Mun rabawa talakawa sama da 75,000 kudi N1.5bn a jihar Kebbi, Ministar Jinkai Sadiya Farouq

A wani labarin kuwa, an damke wasu fastoci biyu, Olumide Peter da Jasulayomi Adetola, kan laifin sauya tunanin mabiyansu domin watsi da iyayensu tare da kona takardun karatunsu saboda Boko Haramun ne.

An gurfanar da su ne a kotun majistaren Ilori ranar Alhamis inda aka cajesu da laifin yaudara, tsorata mutane, boye mutane da kuma damfara.

Alkalin kotun, Ibrahim Dasuki, ya bada umurin garkame Fastocin biyu gidan kason Oke-Kura dake Ilori, Vanguard ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel