Yayinda aka gano wasu a Anambra da Enugu, an sake sace wani yaro a Kano

Yayinda aka gano wasu a Anambra da Enugu, an sake sace wani yaro a Kano

- Kuma dai, an sake sace wani yaro yayinda ya ke komawa gida aga Islamiya a jihar Kano

- Wannan ya biyo bayan gano yaran da aka gano a jihar Enugu da Anambra

- Wannan ba shi ne karo na farko da ake satan yara a Kano ana kaisu wasu jihohi ba

Wani yaro dan shekara 9 da haihuwa, Yusuf Nasiru, dan unguwar Kawaji Quarters a jihar Kano ya bace, yayinda aka gano wasu yaran da aka sace aka kai jihar Anambra da Enugu

Daily Nigerian ta ruwaito cewa sama da yara 12 aka sace a unguwar, wacce tafi fuskantar wannan matsala a jihar Kano.

An yi awon gaba da Yusuf ne a ranar 28 ga Disamba, 2020, yayinda yake hanyar komawa gida daga Islamiyya misalin karfe 6 na yamma.

KU KARANTA: Dokta Bashir: Idan mutum ya saki matarsa a shirin fim to ya saki matarsa ta gida ne

Yayinda aka gano wasu a Anambra da Enugu, an sake sace wani yaro a Kano
Yayinda aka gano wasu a Anambra da Enugu, an sake sace wani yaro a Kano Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Pat Utomi ya siffanta 'yan siyasar arewa da cimma zaune

A ranar Litinin, 11 ga watan Disamba, 2020, gwamnatin jihar Kano ta ce ta gano wasu yara da aka sace aka kai jihar Anambra, Daily Trust ta rahoto wannan.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya shaidawa ‘yan jarida cewa iyayen wasu daga cikin yaran sun gane ‘ya ‘yansu.

Malam Muhammad Garba yace kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa domin gano wadanda aka sace mata ya yi dace, ya gano wasu kananan yara.

Kwamishinan yace an yi nasarar gano wadannan yara ne bayan ‘yan kwamitin sun kai ziyara zuwa gidajen marayun da ke Enugu da Anambra.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng