Trump da mataimakinsa sun yi hannun riga a kan Biden

Trump da mataimakinsa sun yi hannun riga a kan Biden

- Mike Pence, mataimakin shugaban kasar Amurka, ya sanar da cewa zai halarci taron bikin rantsar da Joe Biden

- Hakan na zuwa ne bayan shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa ba zai halrci taron ba

- Amurkawa sun bukaci sauran hadiman gwamnatin Amurka a karkashin jagorancin Pence su tsige Trump

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar Amurka Donald Trump da mataimakinsa, Mike Pence, sun farraka ne a kan batun mika mulki ga zababben shugaban kasar Amurka, Joe Biden.

BBC Hausa ta rawaito cewa an samu rabuwar kai a tsakanin shugabannin bayan Pence ya amince cewa zai halarci wajen taron bikin rantsar da Biden a karshen watan Janairu.

Kafin ya sanar da hakan, Pence ya fara juyawa Trump baya bayan ya bayyana amincewa da nasarar Joe Biden a zaben da aka yi a watan Disamba, 2020.

KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari

Trump da mataimakinsa sun yi hannun riga a kan Biden
Trump da mataimakinsa sun yi hannun riga a kan Biden Hoto: @BBC
Asali: Twitter

Wasu rahotanni sun rawaito Pence na cewa zai halarci wajen taron ne saboda Biden ya aika masa katin gayyata.

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

Tuni shugaba Trump ya saba tsohuwar al'adar kasar Amurka ta hanyar sanar da cewa ba zai halarci taron bikin rantsar da Biden ba.

Legit.ng ta rawaito cewa jagoran 'yan jam'iyyar Democrat a majalisar dattijan kasar Amurka, Chuck Schumer, ya yi kiran a gaggauta tsige Donald Trump saboda rikicin da magoya bayansa suka haddasa ranar Laraba, 6 ga watan Janairu.

A wani jawabi da Schumer ya fitar ranar Alhamis, ya ce 'yan tawayen da suka kutsa cikin Capitol suna da daurin gindin Trump, kamar yadda AP News ta rawaito.

Kazalika, Amurkawa da yawa sun bayyana bacin ransu akan abinda ya faru a Capitol, lamarin da yasa da yawan 'yan kasar ke yin kiran a gaggauta tsige Trump kafin ya kara haddasa wata kitimurmurar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel