Zamu kawo karshen Boko Haram da yan bindiga shekarar nan, shugaba Buhari

Zamu kawo karshen Boko Haram da yan bindiga shekarar nan, shugaba Buhari

- An yi addu'ar zagayowar ranar tunawa da Sojojin Najeriya a Masallacin Abuja

- Shugaba Buhari ya bukaci a taimakawa Sojojin dake faggen fama da addu'a

- Kowace shekara ake bikin tunawa da Sojojin Najeriya da suka mutu a faggen fama

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa za'a kawo karshen ta'addancin da barandanci wannan shekarar ta 2021, a cewar rahoton The Nation.

Ya yi kira ga al'umma su taimakawa sojoji da addu'a domin taimaka musu wajen kawo karshen rikicin.

Shugaban kasa, wanda ya samu wakilcin Ministan tsaro, Bashir Salihi Magashi, a addu'ar ranar tunawa da Sojojin Najeriya da akayi a babban Masallacin tarayya dake Abuja, ya bada tabbacin cewa "wannan shekaran zamu kawo karshen abinda mukeyi."

A cewar Buhari, "abinda ke faruwa a kasar nan zai zo karshe. Wannan shekaran zamu kawo karshen abinda mukeyi; kuyi mana addu'a saboda muyi nasara."

Ya ce kasar nan za ta cigaba da tunawa da jaruntar Sojojin Najeriya kuma za'a cigaba da addu'a Allah ya jikansu bisa sadaukar da rayukansu don kare Najeriya.

Shugaban kasa ya kara da cewa gwamnatin nan za ta cigaba da tabbatar da jin dadin iyalan Sojojin da suka mutu, har da wadanda ke raye.

Limamin Masallacin, Dr Mohammed Kabiru Adam, ya yi addu'a Allah ya jikan matattun Sojin Najeriya.

Hakazalika ya yi addu'an Allah ya kawo karshen wannan rashin tsaro, ta'addanci da sauran abubuwan da suka addabi kasar nan.

KU KARANTA: Daga karshe, Donald Trump ya amince zai sauka daga mulki

Zamu kawo karshen Boko Haram da yan bindiga shekarar nan, shugaba Buhari
Zamu kawo karshen Boko Haram da yan bindiga shekarar nan, shugaba Buhari Hoto: Presidency
Asali: Twitter

DUBA NAN: Trump ya saba tarihi, ba zai halarci bikin rantsar da Biden ba

A wani labarin kuwa, shugaba Muhammadu ya bayyana cewa lallai ya cika alkawarin da yayi wa al'ummar nakasassun Najeriya ta hanyar kafa musu sabuwar ma'aikata.

Buhari ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin mambobin hukumar nakasassun Najeriya.

Mambobin hukumar sun kaiwa shugaba Buhari ziyara ne ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu, 2021, karkashin jagorancin ministar walwala da jinkan jama'a, Hajiya Sadiya Umar Farouq.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel