COVID-19: Zamu saka dokar hana fita - Gwamnatin tarayya tayi barazana

COVID-19: Zamu saka dokar hana fita - Gwamnatin tarayya tayi barazana

- Gwamnatin Buhari na tunanin sake kafa dokar hana zirga-zirga a Najeriya

- Jihohi hudu da akafi kamu da cutar yanzu sune Legas, Kaduna, Abuja da Plateau

- Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasashen da suka samu ba

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ya bayyana cewa gaskiya idan adadin sabbin masu kamuwa da cutar Korona ya cigaba da yawa kamar yadda ake samu yanzu, za'a sake kafa dokar hana fita.

Babban jagoran kwamitin yaki da cutar Korona, Dakta Sani Aliyu, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja, Punch ta ruwaito.

Aliyu yace, "Idan wannan adadin ya cigaba da yawa haka kuma adadin masu mutuwa ya karu, gaskiya babu wata mafita (illa kulle). Idan bamu son a garkame mu, yanzu ne lokacin da ya kamata mubi dokoki."

Hakazalika, shugaban kwamitin, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya ce, "Kwamitin nan na matukar damuwa da yawaitar adadin masu kamuwa da muke samu."

"A ranar 6 ga Junairu, 2021, mun samu mutane 1,664 da suka kamu. Wannan shine mafi yawa tun da ta bulla a Najeriya."

COVID-19: Zamu saka dokar hana fita - Gwamnatin tarayya tayi barazana
COVID-19: Zamu saka dokar hana fita - Gwamnatin tarayya tayi barazana Hoto: Presidency
Asali: Twitter

Kwanaki uku da suka gabata, ministan labarai da al'adu, Lai Mohammed, a jiya ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatin tarayya ba tada niyyar sake kakaba dokar kulle a kasar sakamakon waiwayen korona na biyu.

Ministan wanda yayi jawabi da wani taro a Legas, ya yi kira ga yan Najeriya su bi dokokin da kwamitin fadar shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19 ta gindaya.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari na shirin aron kudaden yan Najeriyan dake ajiye a banki

A bangare guda, mutane 1565 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Alhamis, 7 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 95,934 a Najeriya.

Daga cikin mutane kimanin 96,000 da suka kamu, an sallami 77,982 yayinda 1330 suka rigamu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel