Da duminsa: Daga karshe, Donald Trump ya amince zai sauka daga mulki

Da duminsa: Daga karshe, Donald Trump ya amince zai sauka daga mulki

- Yayinda yan majalisa da wasu ministoci ke bada shawaran tsigeshi, Trump ya saki jawabi

- Ya sake bayyana cewa shi fa bai amince da sakamakon zaben ba amma zai sauka daga mulki

- Ranar 20 ga watan Junairu, 2021 wa'adinsa na shekara hudu zai kare

Daga karshe, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince zai sauka daga mulki kuma ya mikawa Joe Biden bayan majalisar dokoki ta rattaba hannu kan sakamakon zaben.

Amma duk da amincewa da mika mulki, Trump ya jaddada cewa lallai an yi masa magudi ne kuma shi ne sahihin wanda ya lashe zaben.

Ya jaddada cewa bai amince da sakamakon zabe ba, duk da cewa babu wata hujjar da ta nuna cewa an yi magudi.

Jawabin yace: "Duk da cewa sam ban amince da sakamakon zaben ba, kuma ina da hujjoji, zan mika mulki ranar 20 ga Junairu."

"Tuni na lashi takobin cewa ba zamu yarda ba kuma sahihan kuri'u kadai za'a kirga."

"Yayinda wannan ya kawo karshen mulkin shugaba mafi inganci a tarihi, yanzu muka fara yakin sake kara girman Amurka."

KU KARANTA: Atiku Abubakar: Darasin dake cikin zaben shugabancin Amurka

Da duminsa: Daga karshe, Donald Trump ya amince zai sauka daga mulki
Da duminsa: Daga karshe, Donald Trump ya amince zai sauka daga mulki
Asali: Original

KU KARANTA: Sabbin kamuwa da Korona: An samu adadin da ba'a taba samu ba a rana guda

Wannan ya biyo bayan da majalisar dokokin Amurka ta tabbatar da nasarar Joe R Biden Jr a matsayin zababben shugaban kasa bayan nasara kan Donald Trump.

Kidayar kuri'un jihar Vermont ta baiwa Joe Biden adadin kuri'un Electoral College 279 da yake bukata tare da mataimakiyarsa, Kamala Harris.

Majalisar datawar Amurka da na wakilai sun yi watsi da bukatar hana Joe Biden kuri'un Georgia da Pennsylvania.

Bayan haka yan majalisar jam'iyyar Republican sun nuna rashin amincewarsu da kuri'un jihar Arizona, Nevada, da Michigan, amma duka akayi watsi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel