Trump ya saba tarihi, ba zai halarci bikin rantsar da Biden ba
- Yayinda yan majalisa da wasu ministoci ke bada shawaran tsigeshi, Trump ya saki jawabi
- Ya sake bayyana cewa shi fa bai amince da sakamakon zaben ba amma zai sauka daga mulki
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a ranar Juma'a ya sanar da cewa ba zai halarci bikin rantsar da Joe Biden, yayinda ake kira da shi yayi murabus ko a tsige shi ana saura kwanaki 12 da karewar wa'adinsa.
"Ga dukkan wadanda suke tambaya, ba zan halarci rantsarwan ranar 20ga Junairu ba," Trump ya bayyana a Tuwita.
Wannan jawabi ba baiwa mutane mamaki ba daga shugaba mafi raba kan al'umma a Amurka.
Tun shekarar 1869, ba'ayi shugaban kasar Amurka da ya ki halartan taron mikawa wanda zai gajesa mulki cikin mutunci da karramawa ba.
KU KARANTA: Na cika alkawarin da na dauka wa nakasassun yan Najeriya, shugaba Buhari
Mun kawo muku rahoton cewa daga karshe, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince zai sauka daga mulki kuma ya mikawa Joe Biden bayan majalisar dokoki ta rattaba hannu kan sakamakon zaben.
Amma duk da amincewa da mika mulki, Trump ya jaddada cewa lallai an yi masa magudi ne kuma shi ne sahihin wanda ya lashe zaben.
Ya jaddada cewa bai amince da sakamakon zabe ba, duk da cewa babu wata hujjar da ta nuna cewa an yi magudi.
Jawabin yace: "Duk da cewa sam ban amince da sakamakon zaben ba, kuma ina da hujjoji, zan mika mulki ranar 20 ga Junairu."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng