Sabbin kamuwa da Korona: An samu adadin da ba'a taba samu ba a rana guda
- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara
- Adadin wadanda suka kamu ranar Laraba ya kafa sabon tarihi a Najeriya
- Har wa yau Najeriya bata sayo rigakafin Korona daga kasashen da suka samu ba
Mutane 1,664 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 7 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.
Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 94,361 a Najeriya.
Daga cikin mutane sama da 90,000 da suka kamu, an sallami 77,299 yayinda 1324 suka rigamu gidan gaskiya.
Daga cikin wadanda aka sallama ranar Laraba, akwai mutane 388 da sukayi jinya a gidajensu a jihar Legas, mutane 261 a jihar Kaduna, mutane 87 a jihar Plateau, da mutane 20 a jihar Imo.
Wani sabon nau'in cutar Korona da ya samo asali daga Ingila ya shigo Najeriya makonnin bayan nan.
KU KARANTA: Makonni 53 da bullar Korona: Abubuwa 8 da ya kamata ka sani
DUBA NAN: Mutane 1200 sun kamu da cutar Korona a Litinin
Lagos-642
FCT-407
Plateau-160
Kaduna-83
Rivers-62
Adamawa-47
Nasarawa-38
Abia-29
Edo-28
Anambra-27
Niger-24
Ogun-24
Imo-15
Oyo-14
Kano-12
Osun-12
Borno-9
Delta-7
Enugu-7
Bauchi-5
Ekiti-5
Sokoto-5
Jigawa-2
A bangare guda, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19.
Ana ganin cewa shine dan Najeriya na farko da ya karbi rigakafin.
The Cable ta ruwaito mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, ya bayyana hakan ranar Alhamis.
Atiku ya yi nasa alluran ne a Dubai, hadaddiyar daular larabawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng