Casun tambadewa: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sabbin dalilan rushe Otal din Asher

Casun tambadewa: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sabbin dalilan rushe Otal din Asher

- A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya bayar da umarnin rushe Otal din Asher da ke unguwar Barnawa

- 'Yan Nigeria sun bayyana mabanbantan ra'ayi akan rushe Otal din saboda yunkurin shirya wani casu na rashin kunya

- Sai dai, hukumar KASUPDA ta bayar da wasu dalilai na daban da suka sa aka rushe Otal din

Gwamnatin jihar Kaduna ta sake bayar da wasu sabbin dalilan akan rushe Otal din Asher, wurin da aka shirya wani taron casu na badala da tambadewa, kamar yadda The Nation ta rawaito.

A baya an yi tunanin cewa gwamnatin jihar Kaduna ta rushe Otal din ne saboda shirya casun rashin kunya, amma yanzu ta sanar da cewa an gina Otal din ba bisa ka'ida ba.

A makon da ya gabata ne aka cece-kuce a dandalin sada zumunta saboda rushe Otal din Asher saboda yunkurin shirya casun rashin kunya.

Hukumar raya birnin Kaduna (KASUPDA) ta bayyana cewa ta rushe Otal din ne bisa umarnin gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, bisa zargin shirya casun da ya saba da al'adunmu da tarbiya.

KARANTA: Aure ya mutu bayan miji ya kama matarsa tana durawa jaririyarsu yar wata shidda barasa

Da yawan 'yan Nigeria sun yi Alla-wadai da rushe Otal din Asher da KASUPDA ta yi a unguwar Barnawa, ranar 1 ga watan Janairu.

Casun tambadewa: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sabbin dalilan rushe Otal din Asher
Casun tambadewa: Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da sabbin dalilan rushe Otal din Asher
Asali: Facebook

Ana hakan ne sai ga shi KASUPDA ta fitar da sabuwar sanarwar cewa ta rushe Otal din ne saboda rashin cika ka'idojin mallaka da bin tsarin raya birnin Kaduna.

KARANTA: Shekau ya saki faifan sako na farko a cikin 2021, ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi

Hukumar ta ambato wasu tanade-tanade da tsare-tsare da ta ce an saba wajen hatta mallakar filin wurin.

A cewar KASUPDA, akwai kadarori da dama da basu cika irin wadannan ka'idojin ba kuma sannu a hankali za ta cimmasu.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa kimanin mutum 18 ake zargin mahara sun kashe tare da sace wasu matan aure biyu yayin wasu jerin hare-hare a ƙaramar hukumar Giwa dake jihar Kaduna.

A cikin wata sanarwa, Kwamishinan al'amurran cikin gida da sha'anin tsaro, Samuel Aruwa, ya ce farmakin ya faru ne a ƙauyukan Kaya dake da iyaka da Hayin Kaura ta jihar Katsina.

A cewar Kwamishinan, an fara kai hare haren ne tun ranar juma'a lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara, ya kara da cewa cikin waɗanda maharan suka sace harda wata matar aure.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel