Da duminsa: Najeriya ta kara rasa wani farfesa sakamakon Covid-19

Da duminsa: Najeriya ta kara rasa wani farfesa sakamakon Covid-19

- A yau Laraba ne jami'ar jihar legas ta tashi da alhinin rasuwar Farfesa Duro Ajeyalemi

- Ya rasu ne a cibiyar killacewa ta asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas da ke Idi-Araba

- Mataimakiyar shugaban jami'ar jihar Legas, Folasade Ogunsola, ta tabbatar da hakan

Jami'ar jihar Legas da ke Akoka ta tashi a ranar Laraba da alhinin rashin fitaccen Farfesa Duro Ajeyalemi bayan ya kamu da cutar korona.

Marigayin ya yi ritaya daga aiki a jami'ar bayan cikarsa shekaru 70 a watan Nuwamban 2020.

A yayin tabbatar da wannan cigaban ga jaridar Premium times, mataimakiyar shugaban jami'ar da ke lura da lamurran cigaba, Folasade Ogunsola, ta ce hukumar jami'ar ta matukar girgiza da labarin mutuwar.

"Tabbas Farfesa Ajeyalemi ya rasu. Muna cikin mamaki. 'Yan Najeriya su sani cewa cutar korona gaskiya ce kuma su dinga amfani da takunkumin fuska yadda ya dace," Ogunsola ta sanar da manema labarai.

Binciken da Premium Times ta yi ta gano cewa marigayin ya rasu a cibiyar killacewa ne ta asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas da ke Idi-Araba.

KU KARANTA: Baya da Maiduguri, babu inda ke da tsaro a cikin jihar Borno, Farfesa Dikwa

Da duminsa: Najeriya ta kara rasa wani farfesa sakamakon Covid-19
Da duminsa: Najeriya ta kara rasa wani farfesa sakamakon Covid-19. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

KU KARANTA: Kyakyawar budurwa lauya ta ce ta gaji da zama babu miji, tana bukatar wanda za su ci dukiyarta tare (Hotuna)

A wani labari na daban, Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwasoo, dukkansu tsofaffin gwamnonin jihar Kano sun kasance tsoffin makiya a siyasance wadanda basu iya zama a inuwa daya ballantana a siyasa.

Shekarau ya kayar da Kwankwaso a 2003 a lokacin da Kwankwaso yake neman zarcewa. Kwankwaso ya yi nasarar a 2011 inda ya kayar da Salihu Sagir Takai a zaben gwamnoni.

Kwankwaso ya sake nasara bayan Ganduje dan takararsa ya maka Takai dan takarar Shekarau da kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel