Da duminsa: Kotu ta aike Sowore da wasu mutum 4 gidan kurkukun Kuje
- Wata kotun majistare da ke zama a Abuja ta aike Sowore da wasu mutum 4 gidan Kurkukun Kuje
- An gurfanar da su ne sakamakon zanga-zangar da suka fita a Abuja ranar 31 ga watan Disamba
- Ana zarginsa da tada juyin juya hali tare da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Buhari
Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Omoyele Sowore da wasu mutane hudu a gaban wata kotun majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja, jaridar Leadership ta wallafa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ce ta gurfanar da Sowore a kan jagorantar zanga-zangar da suka yi wa gwamnati a ranar 31 ga watan Disamban 2020 a Abuja.
An gurfanar da shi tare da wasu mutane hudu a kan zarginsu da ake da lafifuka uku, lamarin da suka musanta aikatawa.
KU KARANTA: Shugaban PDP da daukacin mabiyansa baki daya sun sauya sheka zuwa APC
Mai gabatar da kara ya zargi masu kare kansu da fara zanga-zanga tare da tada hankali da kuma kira ga juyin juya hali ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Tun kafin nan, Sowore ya yi wata wallafa a shafinsa na Twitter inda ya bukaci jama'a da su fito domin zanga-zanga da nuna fushinsu game da mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Kotun majistaren ta aike Sowore da wasu mutum hudu gidan gyaran hali da ke Kuje a Abuja. Ta ce za ta saurari bukatar bada belinsu a ranar Talata, 5 ga watan Janairun 2020.
KU KARANTA: Rashin tsaro: Fusatattun matasa sun mamaye tare da rufe tituna a Katsina
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum a ranar Asabar ya ziyarci mafarauta shida da a halin yanzu suke karbar kulawar masana kiwon lafiya a asibitin koyarwa da ke Maiduguri.
Mafarautan sun samu miyagun raunika sakamakon dashen abu mai fashewa da mayakan Boko Haram suka yi wanda ya tashi da mafarautan yayin da suke sintiri a dajin Sambisa.
Kusan mafarauta bakwai ne a take suka mutu yayin da wasu 16 suka samu miyagun raunika.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng