Ka hakura kawai; Tanko Yakasai ya fadi dalilin da yasa Tinubu ba zai samu goyon bayan arewa ba a 2023

Ka hakura kawai; Tanko Yakasai ya fadi dalilin da yasa Tinubu ba zai samu goyon bayan arewa ba a 2023

- Alhaji Tanko Yakasai, tsohon dan siyasa kuma tsohon minista, ya yi tsokaci akan zaben shekarar 2023

- Dattijon dan siyasar ya shawarci bangaren kudu maso gabas na 'yan kabilar Igbo akan su zage dantse domin samun tikitin takara

- Kazalika, ya shawarci jagoran jam'iyyar APC, Bola Tinubu, akan ya cire maitar son mulkin shugabancin Nigeria

Dattijo, Alhaji Tanko Yakasai, ya yi tsokaci ga tsarin mulkin karba-karba na shiyya-shiyya akan waɗanda suka cancanci su karɓi mulkin kasar nan a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

A cewar Yakasai, ƙabilar Igbo ba zasu samu mulkin kasar nan ba har sai sun zage damtse, ya ƙara da cewa, Asiwaju Ahmed Bola Tinubu ma ya cire maitarsa ta son sai ya yi mulki a 2023.

Ya ce, tsarin mulkin ƙasar nan ne kaɗai zai bayyana wanda zai karɓi mulki ba tsarin karɓa-karɓa ba wanda bai da tushe cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya ba.

A cewar dattijo Yakasai, banbancen da ke tsakanin al'ummar arewa ya yi yawan da ba zai barsu su yi magana da murya daya ba, a saboda haka Tinubu ya daina saka ran cewa zai samu goyon bayan 'yan arewa kamar yadda ya ke tsammani.

KARANTA: Facebook: Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobarar cewa za ta iya cin amanar aure akan N1m

Yakasai ya kara da cewa Jama'ar arewa da 'yan Nigeria da dama ba zasu goyi bayan Tinubu ba saboda rawar da ya taka wajen kawo mulkin Buhari.

Ka hakura kawai; Tanko Yakasai ya fadi dalilin da yasa Tinubu ba zai samu goyon bayan arewa ba a 2023
Ka hakura kawai; Tanko Yakasai ya fadi dalilin da yasa Tinubu ba zai samu goyon bayan arewa ba a 2023
Source: Original

Ba'a taɓa bayar da mulki a banza ba, tsarin zaɓe ne ke bayarwa. Ina son yan kudu maso gabashin ƙasar nan da su samar da ɗan takarar mai inganci saboda kudu maso yamma sun samar da irinsa; wato Obasanjo.

KARANTA: Harin Jakana ya fusata Zulum, ya yi wa rundunar soji wata tambaya mai muhimmanci

''Kudu maso kudu sun kawo Goodluck yayin da arewa maso yamma suka samar da Yar'adua ga kuma Buhari. Amma a gaskiya tikitin tsayawa takara ba kyauta ba ne. Wajibi ku mike tsaye in kuna so" A cewar Tanko Yakasai.

"Ya ƙara da basu shawara da cewa, "Zabe al'amari ne na janyo hankalin masu kaɗa ƙuri'a ta hanyar gabatar musu da tsare-tsaren ku. Ku gaya musu yadda za ku inganta rayuwarsu. A ƙarshe za su aminta da shi su zabe shi."

A dan haka ya shawarci duk wani da ke son cin zaɓe ta tsarin karɓa-karɓa ciki har da Tinubu, da ya sani ba kundin tsarin mulki ne kuma ba zai yi tasiri ba idan ba aiki suka yi tukuru ba.

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23.

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi

Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel