Dan sandan da ya ki karban cin hancin N864m na shawaran ajiye aiki saboda rashin adalci

Dan sandan da ya ki karban cin hancin N864m na shawaran ajiye aiki saboda rashin adalci

- Bayan shekaru 30, DSP Francis Erhabor na son fita daga hukumar yan sanda

- Erhabor ya bayyana bacin ransa kan irin cin fuska da rashin adalcin da ake yi masa

- Ya shahara da lakabin wanda bai taba karban cin hanci ba a rayuwarsa

Francis Erhabor, DPO na Itam, jihar Akwa Ibom, wanda akwa ruwaito ya ki karban cin hancin N864m a cikin shekaru uku, na tunanin ajiye aikin saboda rashin adalcin da ake masa.

A ranar Asabar, an samu rahotannin cewa DSP Erhabor ya yi murabus daga aikin yan sanda saboda wasu miyagu dake hanashi cigaba a hukumar.

Rahotannin sun bayyana cewa jami'in ya ajiye aikin ne saboda yadda ake karawa sa'o'insa girma amma shi yana waje daya.

Amma daga baya an samu labarin cewa bai yi murabus ba tukun amma yana tunanin yin hakan shi yasa ya dauki hutun kwanaki uku domin yanke shawara, The Cable ta ruwaito.

Jami'in dan sandan ya cika aikin tun shekarar 1990.

KU KARANTA: Jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace

Dan sandan da ya ki karban cin hancin N864m na shawaran ajiye aiki saboda rashin adalci
Dan sandan da ya ki karban cin hancin N864m na shawaran ajiye aiki saboda rashin adalci
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari

A ranar 1 ga Disamba, mun kawo muku rahoton cewa shahrarren dan sandan wanda ake ikirarin bai taba karban cin hanci ba shekaransa 30 yana aiki, ya zama 'Jami'in dan sandan shekara' a zaben lambar yabon Igbere TV 2020.

Yan Najeriya ne suka kada kuri'ar ta yanar gizo. Sun zabi CSP Erhabor ne saboda jajircewarsa da gaskiyansa.

Wannan lambar yabo na Igebere TV yana karrama mutanen da suka fice a wuraren aikinsu.

Kalilan cikin abubuwa ban al'ajabin da yayi sune:

1. Lokacin da yake kwamandan tsare bututun mai a Edo, ya ki karban cin hancin N1.5m da wasu mutane masu fasa bututun mai suka bukaci bashi kowani mako.

2. Ya ki karban N500,000 a kowani mako da abokan aikinsa suke bashi bayan sun karba cin hanci da rashawa daga wajen masu shigo da jabun man fetur cikin jihar.

3. Ya ki karban wadannan kudade duk da cewa kudin alawus dinsa N37,500 ne a wata kuma ba ko yaushe yake samu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng