Dan sandan da bai taba karban cin hanci ba ya zama gwarzon jami'in shekarar 2020

Dan sandan da bai taba karban cin hanci ba ya zama gwarzon jami'in shekarar 2020

- DPO Erhabor ya doke manyan yan sanda 5 a zaben zakaran shekara

- Yan Najeriya da dama sun zabeshi saboda irin jajircewarsa da gaskiya

- Jama'a sun shaida nagartarsa duk da rashin samun albashi mai kyau da alawus

Shahrarren dan sanda wanda ake ikirarin bai taba karban cin hanci ba shekaransa 30 yana aiki, CSP Francis Erhabor, ya zama 'Jami'in dan sandan shekara' a zaben lambar yabon Igbere TV 2020.

Erhabor, wanda yake DPO na D Division, Itam, Uyo, jihr Akwa Ibom, ya lallasa wasu hazikan yan sanda biyar a zaben da aka yi.

Sauran jami'an sune, Frank Mba, Olushola Oyebade, Abba Kyari da Aisha Abubakar.

Yan Najeriya ne suka kada kuri'ar ta yanar gizo.

Wannan lambar yabo na Igebere TV yana karrama mutanen da suka fice a wuraren aikinsu.

Za'a yi bikin mika masa lambar yabonsa ranar 10 ga Disamba, 2020, Vanguard ta ruwaito.

Yan Najeriya sun zabi CSP Erhabor ne saboda jajircewarsa da gaskiyansa.

Misali, inda yake jagoranta, beli kyauta ne kuma babu jami'in dan sandan da ya isa ya karbi cin hanci daga hannun mutan gari.

Hakan ya sa mutan garin aminta da yan sanda kuma suna basu goyon baya da taimako idan suka bukata.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya nada Hajia Imaan Suleiman babbar diraktar hukumar NAPTIP

Kalilan cikin abubuwa ban al'ajabin da yayi sune:

1. Lokacin da yake kwamandan tsare bututun mai a Edo, ya ki karban cin hancin N1.5m da wasu mutane masu fasa bututun mai suka bukaci bashi kowani mako.

2. Ya ki karban N500,000 a kowani mako da abokan aikinsa suke bashi bayan sun karba cin hanci da rashawa daga wajen masu shigo da jabun man fetur cikin jihar.

Ya ki karban wadannan kudade duk da cewa kudin alawus dinsa N37,500 ne a wata kuma ba ko yaushe yake samu ba.

Dan sandan da bai taba karban cin hanci ba ya zama gwarzon jami'in shekarar 2020
Dan sandan da bai taba karban cin hanci ba ya zama gwarzon jami'in shekarar 2020 Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU DUBA: Za'a dawo da Abdulrashid Maina Najeriya daga Nijar, Hukumar yan sanda

A bangare guda, wata kotun Sojoji dake zamanta a Abuja ta kama Manjo Janar Olusegun Adeniyi, tsohon kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, da laifi.

Kotun ta rage masa matsayi da shekaru uku.

Adeniyi, wanda Manjo Janar ne ya bayyana a wani bidiyo a watan Maris inda yake kuka kan rashin makaman yaki da Boko Haram a Arewa maso gabas.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel