Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna)

Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna)

- A karshe, Hukumar KASUPDA ta yi lebur da gidan da aka shirya banbadewa a jihar Kaduna

- Gwamnatin jihar ta ce an rusa gidan tare da damke masu gidan don sun saba dokar hana yaduwar Korona

- Gwamnatin Kaduna ta bada umurnin rufe makarantu sakamakon waiwayen Korona ta biyu

Hukumar yan sandan jihar Kaduna a ranar Alhamis ta bayyana wadanda suka shirya taron banbadewa zindir da aka shirya a shirya kwanakin baya.

Kwamishanan yan sandan jihar, CP Umar Muri, ya bayyana cewa an damke matasan a ranar 27 ga Disamba, 2020, bayan sun yanke shawaran gudanar da casun mai take "Casun lalaci a Kaduna" a wani otel da karamar hukumar Kaduna ta kudu.

Wadanda aka damke sune: Abraham Alber, mammalakin otel din, Umar Rufa'i da Suleiman Lemona, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce babban wanda ya shirya taron ya gudu amma za'a shigar da wadanda aka kama kotu bayan bincike.

Daya daga cikin wadanda aka damke ya bayyana cewa shine ya kawo shawaran taron, amma wasa kawai yake yi tsakaninsa da abokansa.

Ya ce basu shirya casun don tayar da tarzoma a jihar Kaduna ba, kuma ba'ayi don jama'a su gani ba.

"Abin ya fara da wasa ne tsakani na da abokai na, bamu nufi jama'a su gani ba....kawai wata 'yar iya yi ce ta daura a Tuwita," yace.

KU DUBA: Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu

Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna)
Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna) Hoto: @dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa

Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna)
Bayan rusa gudan, an damke wadanda suka shirya casun tsiraici a jihar Kaduna (Hotuna) Hoto: @dailytrust
Asali: Twitter

Gwamnatin Kaduna ta rusa gidan otel ɗin da aka yi shirya gudanar da taron banbadewa zindir farkon makon nan a unguwar Barnawa dake jihar.

Hukumar cigabar cikin garin Kaduna KASUPDA ta bayyana cewa an rusa gidan badalar ne bayan gudanar da bincike kan wajen.

KASUPDA ta bayyana hakan ne a shafinta na Facebook inda ta daura hotunan yadda aka ruwa wajen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel