Wani likita ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan allurar rigakafi

Wani likita ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan allurar rigakafi

- Tuni kasashen duniya, musamman a nahiyar Turai, suka fara amfani da allurar rigakafin cutar korona

- Jama'a da dama, musamman a nahiyar Afrika, na nuna shakku da alamun tambaya a kan allurar rigakafin

- Wani rahoton kafar yada labarai ta BBC ya bayyana yadda wani likita a kasar Amurka ya kamu da koron bayan an yi masara allurar rgakafi

Wani likita da ke aiki a wani asibiti a Jihar California ta kasar Amurka ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan yi masa allurar rigakafi.

Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa an yi likitan allurar rigakafi ta kamfanin Pfizer a makon da ya gabata.

Sakamakon faruwar hakan, kamfanin Pfizer ya bayyana cewa cigaba da bibiyar dukkan wasu bayanai dangane da sabuwar allurar rigakafin.

KARANTA: Ahmad Salkida: A yanar gizo na ga faifan bidiyon da 'yan Boko Haram suka kashe 'yan uwana, ni ma sun gargadeni

"Rigakafin na bukatar lokaci kafin ta ginu a jikin mutum, mutum zai iya kamuwa da kwayar cutar kwanaki goma kafin ko bayan yi masa allurar rigakafin," a cewar wata sanarwa da kamfanin ya fitar.

Wani likita ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan allurar rigakafi
Wani likita ya kamu da kwayar cutar korona sati daya bayan allurar rigakafi
Asali: UGC

A ranar 18 ga watan Disamba ne likitan mai suna Matthew W., dan shekaru 45, ya sanar da cewa an yi masa allurar rigakafin korona ta kamfanin Pfizer.

KARANTA: An fara gulma da tsegumi akan dalilin ganawar Buhari da Zulum a Villa

A lokacin, Matthew ya bayyana cewa bayan ciwon wuni guda da hannunsa ya yi, allurar ba ta da wata illa.

A ranar Lahadi, 27 ga watan Disamba, ne Legit.ng ta rawaito cewa cutar korona ta hallaka tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a mulkin soji, Air Commodore Idongesit Nkanga.

Kafin rasuwarsa, Nkanga shine shugaban kungiyar kishi da son cigaban yankin Neja-Delta (PANDEF)

Marigayi Nkanga ya shugabanci jihar Akwa Ibom daga shekarar 1990 zuwa shekarar 1992 a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa a mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng