Ahmad Salkida: A yanar gizo na ga faifan bidiyon da 'yan Boko Haram suka kashe 'yan uwana, ni ma sun gargadeni

Ahmad Salkida: A yanar gizo na ga faifan bidiyon da 'yan Boko Haram suka kashe 'yan uwana, ni ma sun gargadeni

- Ahmad Salkida, dan jarida kuma dan asalin Jihar Borno, ya dade cikin zargin cewa yana da alaka da kungiyar Boko Haram

- Sai dai, matashin dan jaridar ya sha musanta wannan zargi tare da bayyana cewa shi ma bai tsallake sharrin kungiyar ba

- A wani sako da ya wallafa ranar Laraba, Salkida ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sun kashe wasu 'yan uwansa

Matashin dan jarida, Ahmad Salkida, dan asalin jihar Borno ya koka akan yadda har yanzu wasu mutane da hukumomi ke zarginsa da alaka da kungiyar Boko Haram.

Salkida, mai kamfanin jaridar yanar gizo ta "HumAngle" ya taba yin gudun hijira zuwa ketare sakamakon fuskantar matsin lamba, kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana.

Dan jaridar na yawan kare kansa tare da ganin baiken masu alakanta shi da kungiyar Boko Haram ko Kuma watsa labaransu.

KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun koma cikin fushi bayan guduwar mutane 8 da suka sace, sun sake sace wasu 9

A wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita domin kare kansa, Salkida ya bayyana cewa shi ma bai tsallake kaidin kungiyar Boko Haram ba.

A cewar Salkida, a yanar gizo ya ga faifan bidiyon kisan gillar da mayakan kungiyar Boko Haram suka yi wa wasu 'yan uwansa na jini.

KARANTA: An fara gulma da tsegumi bayan fadar shugaban kasa da gwamna Zulum sun yi gum a kan ganawarsu

Kazalika, ya bayyana cewa shi da kansa Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram, ya ambaci sunansa tare da yi masa barazana.

Ahmad Salkida: A yanar gizo na ga faifan bidiyon da 'yan Boko Haram suka kashe 'yan uwana, ni ma sun gargadeni
Ahmad Salkida: A yanar gizo na ga faifan bidiyon da 'yan Boko Haram suka kashe 'yan uwana, ni ma sun gargadeni
Asali: UGC

Salkida ya nuna takaicin yadda duk da hakan wasu sun gaza fahimta, sun ki yarda cewa bashi da wata nasaba, ta zahiri ko badini, da kungiyar Boko Haram.

Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga 'yan Najeriya tare da kalubalantar Buhari da shugabanni akan su daina dorawa Allah laifin rashin cigaban kasa.

Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.

Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: