An tafka magudi, a sake sabon lale; Tsohon shugaban kasar Ghana ya yi watsi da sakamakon zabe

An tafka magudi, a sake sabon lale; Tsohon shugaban kasar Ghana ya yi watsi da sakamakon zabe

- Tsohon shugaban kasar Ghana kuma jagoran 'yan adawa, John Mahama, ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa

- Dattijo Mahama na son kotu ta tilastawa hukumar zabe janye sanarwar cewa Akufo-Addo ne ya samu nasara

- Duk da rundunar 'yan sanda ta sanar da mutuwar mutane biyar, masu sa'ido sun ce an yi adalci a zaben

Jagoran yan adawa a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a kasar Ghana, John Mahama, ya shigar da ƙara inda ya buƙaci kotu da ta tursasa hukumar zabe ta sake gudanar da sabon zaɓe karo na biyu.

Channels ta rawaito cewa Mahama ya bayyana cewa sanar da Akufo-Addo a matsayin wanda lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 9 ga watan Disamba ba dai-dai ba ne ta kowacce fuska.

Mahama, mai shekaru 62, na son kotu ta haramtawa Akufor-Addo nasarar da ya samu ta zama sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Ghana wanda hukumar zaben ƙasar ta ayyana shine wanda ya lashe zaben da kaso 51.59%.

KARANTA: Korona 2.0: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria

An tafka magudi, a sake sabon lale; Tsohon shugaban kasar Ghana ya yi watsi da sakamakon zabe
An tafka magudi, a sake sabon lale; Tsohon shugaban kasar Ghana ya yi watsi da sakamakon zabe @Channels
Source: Twitter

A zantawarsa da manema labarai, Mahama ya ce, "Yadda nake a tsaye gabanku, ina mai kara jaddada muku cewa ba za mu amince da sakamakon wannan zaɓen mai cike da magudi ba, za mu bi duk wata halastacciyar hanya don tabbatar da cewa mun samu adalci."

KARANTA: Pantami Vs Dabiri, Malami Vs Magu da wasu sabani 3 da aka samu tsakanin hadiman Buhari

Masu sa-ido a ciki da wajen Ghana sun bayyana cewa zaɓen dai an yi shi cikin adalci. Sai dai, 'yan sandan ƙasar sun bayyana cewa an kashe mutum biyar sannan mutane 19 sun ji rauni.

A gida Nigeria, Legit.ng ta rawaito cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga 'yan Najeriya tare da kalubalantar Buhari da shugabanni akan su daina dorawa Allah laifin rashin cigaban kasa.

Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.

Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel