WHO ta gargadi duniya akan bullar wata annoba da ta fi korona hatsari

WHO ta gargadi duniya akan bullar wata annoba da ta fi korona hatsari

- Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce akwai yiwuwar bullar wata annoba da ta fi korona karfi da hatsari

- A cewar WHO, duk da annobar korona ta girgiza duniya, babbar annobar na nan tafe, kamar yadda Dr.Mike Ryan ya bayya

- Annobar korona ta kama sama da mutan miliyan 82.6 a faɗin duniya inda sama da mutum miliyan 1.8 suka riga mu gidan gaskiya tare da kassara tattalin arzikin duniya

Hukumar Lafiya Ta Duniya, WHO, ta yi gargaɗi duniya baki daya da a shiryawa bullar wata ƙwayar cutar da ta fi COVID-19 hatsarin gaske da ka iya kawar da duniya baki daya, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Shugaban hukumar ɓangaren shirye-shiryen agajin gaggawa, Dr Mike Ryan ya bayyana haka ranar Laraba yana mai cewa COVID-19 mummunar cuta ce, amma akwai wacce ta fi ta, kuma tana nan zuwa.

A cewar ta bakin Dr Ryan, lokacin da yake ganawa da yan jarida ya ce corona "Kawai mai sharar fage ce.

Mu na koyon yadda za mu yi abubuwan ne da kyau, daga: kimiyya, rarraba kayayyaki, horaswa da sadarwa su zama sun inganta. Amma gaskiya duniyar nan bata da tabbas.

KARANTA: Pantami Vs Dabiri, Malami Vs Magu da wasu sabani 3 da aka samu tsakanin hadiman Buhari

"Muna rayuwa cikin zamantakewa iri-iri. Wannan barazana za ta cigaba. Idan akwai abu daya da za mu koya daga wannan annobar, shine aiki tare. Yana da kyau kuma mu karrama waɗanda muka rasa ta sanadiyar yaƙi da wannan annobar".

WHO ta gargadi duniya akan bullar wata annoba da ta fi korona hatsari
WHO ta gargadi duniya akan bullar wata annoba da ta fi korona hatsari
Asali: UGC

Dr Ryan ya ƙara da cewa "Wannan annobar ba ƙaramar masifa ba ce, ta girgiza kowanne ɓangare na duniya. Amma ku sani, wannan ba ita ce babbar annobar ba."

KARANTA: 'Yan bindiga sun koma Sabuwa cikin fushi bayan guduwar mutanen da suka sace, sun sake sace wasu 9

Cutar korona dai ta kama sama da mutan miliyan 82.6 a faɗin duniya inda sama da mutum miliyan 1.8 suka riga mu gidan gaskiya tare da kassara tattalin arzikin duniya.

A yanzu haka dai ana rarraba miliyoyin magungunan riga-kafin wannan cutar da aka yi nasarar samu wanda hukumar lafiya kuma ta amince da ingancinsu.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta fidda sanarwar ƙaryata neman afuwar Shugaba Buhari bisa gayyatarsa ya gurfana gaban majalisar don bayani kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.

Sanarwar ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke fitarwa kan cewar ƴan majalisar za su roƙi afuwar Shugaban ƙasa bayan sun amince da ƙudirin gayyatarsa, kamar yadda BBC ta wallafa.

Wasu ƴan majalisa daga jihar Borno ne suka nemi a gayyato shugaba Buhari don ya yi bayani akan halin rashin tsaro da ake fama da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng