Yanzu-yanzu: Yan Majalisar dattawa sun kammala aiki kan kasafin kudin 2021, sun yi kari sama da N500bn
- Yan majalisar dattawan tarayya sun gama kanikancin kasafin kudin 2021, Sanata Barau Jibrin ya bayyana
- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin gaban majalisa a watan Oktoba
- Sanata Ahmed Lawan ya bayyana amincewar majalisar da kasafin kudin 2021 tare da karin sama da bilyan 500
Majalisar dattawa Najeriya ta amince da kasafin kudin N13.588 tiriliyan na shekarar 2021 da shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar watanni biyu baya yanzu.
Hakan ya biyo bayan kammala aikin da kwamitin lissafe-lissafen kasafin kudi da tayi kan kasafin kudin.
Shugaban kwamitin, Sanata Barau Jibrin, ya gabatar da daftarin kasafin kudin a ranar Litinin, 21 ga watan Disamba, 2020.
Yan majalisar sun yi karin sama da biliyan 500 kan abinda shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar.
A watan Oktoba, Buhari ya gabatar da kasafin N13.08tr amma yanzu an mayar da shi N13.588tr
Asali: Legit.ng