Zakzaky da wasu fitattun mutum 3 da suka yi Kirsimeti a gidan yari

Zakzaky da wasu fitattun mutum 3 da suka yi Kirsimeti a gidan yari

- Ana yin biki tare da shagalin Kirsimeti a ranar 25 ga watan Disamban kowacce shekara

- Yayin da ake shagalin, wasu fitattun 'yan Najeriya na garkame a gidan kurkuku

- Wasu daga ciki an yanke musu hukunci yayin da wasu suke jiran a kammala shari'a

Kirsimeti biki ne tare da shagali da ake yi duk karshen shekara amma ga mabiya addinin Kirista. An yi shagalin a ranar Juma'a 25 ga watan Disamban 2020.

Amma a yayin da wasu 'yan Najeriya ke cikin wannan walwalar, wasu fitattun suna gidan kurkuku a daure.

Daga cikin fitattun 'yan Najeriyan da ke gidan kurkukun kuwa akwai wadanda ke fuskantar shari'a ko kuma aka yanke musu hukunci.

Legit.ng ta lissafo wasu fitattun mutane 4 da ke daure yayin bikin Kirsimeti.

Zakzaky da wasu fitattun mutum 3 da suka yi Kirsimeti a gidan yari
Zakzaky da wasu fitattun mutum 3 da suka yi Kirsimeti a gidan yari. Hoto daga Sahara Reporters
Asali: UGC

KU KARANTA: Gara in yi wufff in shige a mata ta 7 da in yi alakar banza, 'Yar kasuwa tare da Ned Nwoko

1. Abdulrasheed Maina

An mayar da Maina gidan yari bayan an kama shi a kasar Nijar inda ya tsere bayan bada belinsa. Hakan yasa kuwa aka cafke sanata Ndume da ya tsaya har aka bada belin.

Tsohon shugaban hukumar fanshon yana fuskantar shari'a a kan laifuka 12 da suka hada da handamar makuden kudaden hukumar.

2. Ibrahim El-Zakyzaky

Shugaan kungiyar musulmi mabiya Shi'a (IMN) ya kasance a gidan yari tun 2015 inda aka damke shi tare da matarsa Zeenat bayan tarzomar da mabiyansa suka tada wa sojin Najeriya.

Duk da kotu masu yawa sun bukaci a sakesa tare da matarsa, wannan Juma'a da ta gabata ne shugaban kungiyar yayi Kirsimeti ta shida a garkame.

3. Joshua Dariye

An yanke wa tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye hukunci a watan Yunin 2018 a kan wata gagarumar damfara.

Wata babbar kotu da ke Abuja ta yanke masa hukuncin shekaru 16 a gidan maza amma kotun daukaka kara ta mayar masa da shekaru 4.

KU KARANTA: Babu shakka Najeriya za ta tarwatse matukar ba a dauka wannan matakin ba, Fitaccen shugaba a Arewa

4. Jolly Nyame

Jolly Nyame tsohon gwamnan jihar Taraba ne da aka yanke wa hukunci a kan damfarar N1.64 biliyan a cikin zargi 41 da EFCC take masa.

Duk da Nyame ya ce zai mayar da kudin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke masau shekaru 14 a gidan maza.

A wani labari na daban, a halin yanzu, majalisar wakilai bata da bukatar ganawa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa a kan matsalar tsaro da ya addabi fadin kasar nan, jaridar The Nation ta tabbatar da hakan a ranar Asabar.

Shugaban majalisar kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, ya gano cewa gayyatar farko ta koma ta kabilanci da siyasa.

An gano cewa wasu 'yan majalisar da suka assasa gayyatar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bai wa fadar shugaban kasan hakuri.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel