Budurwa ta sayar da gonar mahaifinsu ta bawa saurayi kudin don ya fita turai karo karatu

Budurwa ta sayar da gonar mahaifinsu ta bawa saurayi kudin don ya fita turai karo karatu

- Wata matashiyar budurwa a jihar Delta ta sayar da gonar mahaifinsu tare da bawa saurayinta kudin don ya karo karatu a waje

- Budurwar, kamar yadda dan uwanta mai suna Joseph ya bayyana, ta sayar da gonar ba tare da sanin kowa ba

- Mahifin budurwar mai suna Mista Ekpo ya yi barazanar kashe diyar tasa tare da saurayinta

Ana zargin matashiyar budurwa da sace takardun gonar mahaifinsu ba tare da ya sani ba, ta hanyar sauya sunan mai mallaka tare da sayar da ita a matsayin ita ce mai gonar.

Saurayin budurwar ne ya samu gurbin yin digiri na biyu a jami'ar Aberdeen sai dai ba shi da isassun kuɗaɗe, lamarin da ya sa budurwar tasa ta yanke shawarar sayar da gonar mahaifin nata don taimaka masa, a cewar dan uwanta, Joseph.

KU KARANTA KUMA: Kukah: Ban yi kira ga juyin mulki a kan gwamnatin Buhari ba, limamin Katolika ya fayyace gaskiya

Budurwa ta sayar da gonar mahaifinsu ta bawa saurayi kudin don ya fita turai karo karatu
Budurwa ta sayar da gonar mahaifinsu ta bawa saurayi kudin don ya fita turai karo karatu Hoto: nigerianscholars.com
Asali: UGC

Daga baya ne dai mahaifin ya gano cewa an sayar masa da gonarsa bayan da ya kai ziyara inda wanda ya saya ya nuna masa hakikanin takardun mallakar gonar.

Wannan lamari dai ya yi matuƙar fusata mahaifin mai suna Mista Ekpo, mazaunin jihar Delta, inda ya yi barazanar kashe ta ita da saurayin nata.

Ko da aka tuntubi yarinyar, ba ta musanta sayar da gonar ba don tallafawa karatun saurayin nata wanda ya fuskanci matsalar rashin kuɗi don karo karatu a ƙasar waje.

KU KARANTA KUMA: Shugaban kasa 2023: Primate Ayodele ya ce Allah bai aiko Tinubu don ya shugabanci Najeriya ba

A wani labarin, wata mata 'yar kasuwa daga kasar Zambia ta ce a maimakon zaman haka gara ta shiga a matsayin mace ta bakwai tunda ta san matsayinta da kuma soyayyar da ake mata, a kan ta kasance da wanda bai dace ba sannan babu mutunci.

Phyllis Thompson ta sanar da hakan ne a wata wallafa da tayi a shafinta na Facebook tare da wallafa hotunanta tare da mijin Regina Daniels, Ned Nwoko.

Ta kara da cewa hankalinta ya dauku da neman kudi kuma yadda ake mutunta ta tamkar sarauniya yasa bata bukatar komai a rayuwarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel