Gara in yi wufff in shige a mata ta 7 da in yi alakar banza, 'Yar kasuwa tare da Ned Nwoko
- Wata mata 'yar kasuwa daga kasar Zambia ta wallafa hotunanta tare da biloniya Ned Nwoko
- A wallafar ta ce gara ta shiga a mace ta 7 domin ta san matsayinta kuma ana son ta aka aura
- Ta ce alaka mara kyau wacce babu mutunci a ciki tare da zargi bata dace da mace kamar ta ba
Wata mata 'yar kasuwa daga kasar Zambia ta ce a maimakon zaman haka gara ta shiga a matsayin mace ta bakwai tunda ta san matsayinta da kuma soyayyar da ake mata, a kan ta kasance da wanda bai dace ba sannan babu mutunci.
Phyllis Thompson ta sanar da hakan ne a wata wallafa da tayi a shafinta na Facebook tare da wallafa hotunanta tare da mijin Regina Daniels, Ned Nwoko.
Ta kara da cewa hankalinta ya dauku da neman kudi kuma yadda ake mutunta ta tamkar sarauniya yasa bata bukatar komai a rayuwarta.
KU KARANTA: Bidiyon lokacin da Buhari ya hadu da sojan da ya fi kowa tsayi a dakarun Najeriya
Kamar yadda ta wallafa, "Gara in kasance da auren mai mata kuma in san matsayina sannan a so ni, mutunta ni tare da bani kariya a maimakon alaka da mutanen da bai dace ba sannan babu mutunci.
"Ina fama da ayyukan kuma ana mutunta ni tamkar sarauniya. Bana bukatar komai a rayuwata. Ina bi ta kan abinda ya dameni. Idan kina yin abubuwan da suka dame ki tare da cigaba a rayuwarki, baki da lokacin duk wani rikici."
KU KARANTA: Miyagu sun halaka mutum 7, sun kone mota dankare da buhunan masara a Kaduna
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana matukar shiga takaici da bakin ciki in har aka samu rashin zaman lafiya da karantsaye a kan tsaro a kasar nan.
Shugaban kasan a sakonsa na Kirsimeti ga 'yan Najeriya ya yi kira garesu da su bada goyon baya ga dakarun soji da sauran hukumomin tsaro.
"Da gangan ba zan ki sauke babban nauyin da ke kaina ba na tabbatar da tsaron rayuka da kadadrori ba. Ina shiga halin takaici matukar aka samu karantsaye a fannin tsaron kasar nan."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng