An samu sauki: Mutane 397 suka kamu da cutar Korona ranar Litinin

An samu sauki: Mutane 397 suka kamu da cutar Korona ranar Litinin

- Ko shakka babu yanzu, an shiga babin annobar korona 2.0

- Bayan fiye da mako daya jere, an samu adadin sabbin masu kamuwa kasa da 500 a rana

- Gwamnati ta bada umurnin rufe makarantu, gidajen biki, gidajen rawa kuma an dakatad da bukukuwan Kirismeti

Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria sun nuna cewa ko shakka babu an koma gidan jiya.

Mutane 397 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Litinin, 29 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Litinin ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 84,811 a Najeriya.

Daga cikin sama da mutane 80,000 da suka kamu, an sallami 71,357 yayinda 1264 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila

An samu sauki: Mutane 397 sukakamu da cutar Korona ranar Litinin
An samu sauki: Mutane 397 sukakamu da cutar Korona ranar Litinin Crdit: @NCDCgov
Asali: Twitter

KU KARANTA: ‘Yan Majalisa sun mikawa Buhari kundin kasafin kudin 2021 domin ya sa hannu, shiru

Ga jerin jihohin da adadin wadanda suka kamu:

Lagos-144

Plateau-83

Kaduna-48

Adamawa-36

Rivers-22

Oyo-16

Kebbi-10

Nasarawa-7

Sokoto-7

FCT-5

Kano-5

Edo-4

Jigawa-3

Ogun-2

Akwa Ibom-2

Niger-1

Bauchi-1

Zamfara-1

A bangare guda, Shugaba Cyril Ramaphosa a ranar Litinin ya sanar da sabuwar dokar hana siyar da giya ya kuma ce wajibi ne amfani da takunkumin fuska a wajen taron jama'a bayan Kasar Afirka ta Kudu ta zama ta farko a nahiyar Afirka da ta kai mutane miliyan daya da suka kamu da Coronavirus.

Ramaphosa ya zartar da sababbin sharadai saboda "yawan karuwar" masu cutar, musamman ganin cewa barkewar cutar karo na biyu na iya zama mai munin gaske

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng