Suna da Ofis: Rundunar 'yan sanda ta nada sabbin DIG biyar
- Babban sifetan rudunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya nada sabbin manyan mataimakansa
- Kazalika, ya bayar da gurbin aiki ga kowanne daga cikin manyan jami'an guda biyar da aka nada mukamin DIG
- IGP Adamu ya bukaci sabbin manyan 'yan sandan su yi aiki da kwarewarsu ta aiki wajen kawo sauyi mai ma'ana a rundunar 'yan sanda
Insifekta janar na rundunar yan sandan ƙasar nan, IGP Mohammed Adamu, ya ba da umarni tura sabbin manyan jami'an yan sanda biyar waɗanda aka yiwa karin girma zuwa manyan mataimakan IG (DIG) zuwa wuraren aiki.
Mohammed Adamu ya bayar da umarnin ne ranar Juma'a ne don rarraba sabbin jami'an da suka samu karin girma don maye gurbin tsaffin jami'an yan sanda da suka yi ritaya.
Wannan na kunshe ne a cikin takardar da mai magana da yawun hukumar ta yan sanda, Frank Mba, ya rabawa manema labarai a Abuja.
KARANTA: Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya
Bayanin kunshin takardar na cewa "DIG Usman Alkali Baba, zai tafi ɓangaren binciken laifuka, DIG Ibrahim A. Lamorde; ɓangaren kwararru na musamman, DIG David Oyebanji Folawiyo; ɓangaren sadarwa da muhimman bayanai, DIG Dan-Mallam Mohammed; ɓangaren horaswa da cigaba, sai kuma DIG Joseph O. Egbunike, ɓangaren sha'anin kuɗi da mulki."
A takardar, IG ya taya sabbin manyan yan sanda murnar ƙarin girman da suk samu tare da tuna musu cewa su yanzu suna cikin manyan ma'aikata na rundunar.
KARANTA: Akwai maganar tsige Buhari a majalisa; dan majalisa ya tona asiri
Kazalika, ya kuma shawarcesu da su nuna kwarewa da sanin aiki don kawo shuagabanci nagari a rundunar 'yan sanda.
A baya Legit.ng a rawaito cewa wani mamba a majalisar wakilai ta tarayya na gab da shiga tsaka mai wuya sakamakon kiran da ya yiwa majalisar da ta tsige shugaban ƙasa bisa gazawa wajen samar da tsaro a Najeriya.
Dan majalisar wakilan, Kingsley Chinda, mai wakiltar Obia/Akpor kuma ɗan jam'iyyar PDP, ya bukaci da a tsige shugaba Muhammadu Buhari ranar 7 ga Disamba biyo bayan yankan rago da yan kungiyar Boko Haram ta yiwa wasu manoma a Zabarmari.
Kazalika, ya ce bai kamata a bar batun kin bayyanar da shugaban kasar ya yi a zauren Majalisar don karin bayani kan taɓarbarewa tsaro ta wuce haka ba.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng