Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje

Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje

- Wani matashi ya bada labarin yadda budurwa 'yar Najeriya ta yaudari abokinsa dan Najeriya

- Ya bada labarin yadda saurayin ya samar mata da visa tare da kanwarta suka lula ketare

- Tana isa ta samu wani saurayi wanda ta manne wa tare da yin watsi da tsohon saurayin

Wata budurwa 'yar Najeriya ta yi watsi da saurayinta da yayi mata visa tare da daukar nauyinta ta yi karatu har jami'a.

Wani Shadrack Okpomhe wanda ke aiki da kungiyar Edo Diaspora Organization, a ranar Laraba 23 ga watan Disamba, ya bada labarin yadda budurwar ta nemi taimakon saurayin domin samun Visa.

Saurayin bai yi kasa a guiwa ba ya kira Shadrick domin neman yadda za su yi tare da wata kanwarta domin samun visa.

Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje
Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon dan Najeriya sanye da babban riga ana rantsar da shi a Amurka bayan ya lashe zabe

"A shekaru kadan da suka gabata, an tuntube ni domin samun visa na wata budurwa, wanda ni kuma na samo. An ba su dukkan takardun bayan kammala komai,"

"Mahaifiyar saurayin ta gane abinda ke faruwa kuma bata yi na'am da lamarin ba. Amma kuma sai saurayin ya rike wuta ya ba budurwar taimakon da take bukata.

"Bayan makonni kadan, budurwa da kanwarta suka shilla kasar waje sannan ta samu sabon saurayi."

"Abun takaici shine yadda budurwar ta manne da wani saurayi ta bar saurayinta na Najeriya. Abun ya matukar tada min hankali tare da bata min rai," ya wallafa.

Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje
Budurwa ta yi watsi da saurayinta bayan ya dauki nauyin karatun ta a kasar waje. Hoto daga Shadrack Okpombe
Asali: Facebook

KU KARANTA: Rahoto: Yaran makarantan Kankara sun fallasa FG, sun bayyana hanyar da aka bi aka cece su

A wani labari na daban, wasu 'yan bindiga a ranar Laraba da yammaci sun kai wa dakarun soji hari a karamar hukumar Okene ta jihar Kogi inda suka kashe sojin ruwa biyu.

Jaridar Tribune Online ta tabbatar da cewa an kai wa sojin hari wurin karfe 7 na yammacin ranar Laraba a Okene yayin da suke shirin fara aiki.

Shugaban karamar hukumar Okene, Abdulmumin Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng