Gyara kayanka: Pius Anyim ya fadi halayyar da 'yan kabilar Igbo zasu gyara idan suna son mulki a 2023

Gyara kayanka: Pius Anyim ya fadi halayyar da 'yan kabilar Igbo zasu gyara idan suna son mulki a 2023

- Anyim Pius Anyim, tsohon shugaban majalisar dattijai, ya ce sai 'yan kabilar Igbo sun sauya halayyarsu kafin su iya samun takarar kujerar shugaban kasa

- Tsohon Sanatan ya ce mutanen yankin kudu maso gabas, na 'yan kabilar Igbo, basa son fitowa kada kuri'a yayin zabe

- Ya ce dole kungiyoyin yankin su tashi tsaye wajen wayar da kan jama'a a kan muhimmanci fitowa kada kuri'a yayin zaben kujerar shugaban kasa da sauran zabuka

Tsohon shugaban majalisar dattijai, Anyim Pius Anyim, ya ce yankin kudu maso gabashin kasar nan, shine yankin da ya fi kowanne yanki ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri'a lokacin zaben kujerar shugaban kasa.

Sanata Anyim, ya yi wannan iƙirari ne a wani biki mai taken World Igbo Summit, wanda jami'ar Gregory dake Uturu a jihar Abia ta shirya a karo na shida, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Cikin bayaninsa mai taken, "Duban tsanaki kan buƙatar ƙabilar Igbo ga mulkin ƙasar nan tare da tsarin cimma hakan," Anyim ya nuna giɓin dake akwai na ɓallewa ko sauya tsarin fasalin ƙasar nan.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Gyara kayanka: Pius Anyim ya fadi halayyar da 'yan kabilar Igbo zasu gyara idan suna son mulki a 2023
Gyara kayanka: Pius Anyim ya fadi halayyar da 'yan kabilar Igbo zasu gyara idan suna son mulki a 2023
Asali: UGC

Domin cimma wannan buƙata, sanata Anyim, ya ce: "Tabbas abu ne mai samuwa idan aka bi abin a tsare cikin haɗin kan kowa.

"Amma abu mafi muhimmanci ga yankin na Igbo, akwai buƙatar wayar da kai da kuma ƙara yawan masu fitowa kaɗa ƙuri'a.

KARANTA: Korona: El-Rufa'i ya dauki sabon mataki da ya shafi ma'aikata, Masallatai, da Cocinan Kaduna

"Yankin Kudu maso gabashin kasar nan dole su sauya tsari, su ke fitowa suna kaɗa ƙuri'a lokacin zabe.

"Kungiyoyi, kamar irin World Igbo Summit, suna da gudunmawar da za su bayar ta karfafa guiwa da wayar da kan masu kaɗa ƙuri'a," a cewarsa.

Tsohon sanatan ya kara kira ga daidaikun kungiyoyin dake yankin da su himmatu wajen samun nasarar wannan babban buri da suke son cimma.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa neman wa'adin mulki na biyu ga shugaban jam'iyyar PDP, Prince Uche Secondus, ya gamu da gagarumin tasgaro.

Hakan ya biyo bayan alamu da gwamnoni tsagin jam'iyyar ta hamayya ke nunawa akan cewa wataƙila ko za su sauya shi dab da ƙaratowar zaɓen 2023.

An gano cewar gwamnonin suna son Secondus, ɗan asalin jihar Rivers, ya sauka daga kujerar bayan ficewar gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi zuwa APC.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng