Zulum ya bankado ma'aikatan bogi fiye da 20,000 a Jihar Borno
- Farfesa Babagana Umar Zulum, gwamnan Borno, ya bankado ma'aikatan bogi da fiye da dubu ashirin
- Daga cikin jimillar ma'aikatan bogi 22,556 da kwamitin tantancewa ya gano, akwai malaman makaranta da ma'aikatan kananan hukumomi
- Gwamna Zulum ne ya fadad binciken tantance zuwa matakin karamar hukuma da makarantun firamare da ke fadin jihar Borno
Gwamnatin jihar Borno ta bankaɗo malaman bogi da ma'aikatan ƙananun hukumar dake jihar kimanin 22,556 a wani yunkurin tantance ma'aikata da malamai da gwamnan jihar, Farfesa Babagana Zulum, ya bayar da umarnin aiwatarwa.
Alƙaluman sun nuna kimanin ma'aikatan bogi 14,662 aka gano a ƙananun hukumomin jihar yayin da aka gano wasu malaman karya har 7,794 a ɓangaren ilimi.
Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin tantance malaman firamare, Dr. Shettima Kullima, ya ce, tantancewar ta samarwa jihar rarar kuɗi sama da miliyan 183 da suke zurarewa a iya ɓangaren malaman firamare kaɗai dake ƙananun hukumar 27 dake faɗin jiha.
Bayan karɓar rahoton ne kuma gwamna Zulum, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne don inganta harkar ilimi a jihar Borno, kasancewar gwamnatinsa ta baiwa harkar ilimin firamare fifiko.
KARANTA: An kama 'Ahmed Musa' na bogi da laifin damfarar N700,000 a Kano
An fara tantance ma'aikata a jihar ta Borno tun a shekarar 2013 inda aka samo dubbanin ma'aikatan bogi.
Gwamna Zulum ne ya yanke shawarar faɗaɗa tantancewar har zuwa ma'aikatan ƙananun hukumomin jihar Borno guda ashirin da bakwai.
A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa gwamna Zulum ya ratsar da sabbin zababbun shugabanninn kananan hukumomin jihar Borno 27.
Daga cikin sabbin shugabannin kanananan hukumomin da aka rantsar akwai Farfesoshi biyu da wani mai digiri da digirgir (PhD).
Kazalika, Farfesa Zulum ya bayar da umarnin sakarwa kananan hukumomin jihar Borno dukkan kudadensu kamar yadda dokar kasa ta bukata.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng