Korona 2.0: Hadimin Buhari ya nuna yiwuwar dawowar dokar kulle a karo na biyu

Korona 2.0: Hadimin Buhari ya nuna yiwuwar dawowar dokar kulle a karo na biyu

- Duk da sanar da cewa an samu rigakafin annobar kwayar cutar korona, har yanzu annobar ba ta daina firgita duniya ba

- Tuni jihohin Nigeria da dama suka sanar da sake rufe makarantun firamare da sakandire domin dakile yaduwar kwayar cutar

- Kazalika, an rufe manyan wuraren taron jama'a, musamman domin biki ko nishadi, tare da bawa wuraren ibada sabbin dokoki

Bashir Ahmad, mai taimakawa shugaban ƙasa Muhammad Buhari akan harkokin yaɗa labarai, ya nuna akwai yiwuwar sake dawo da dokar kulle a ƙasa, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Tuni dai wasu jihohi suka yi umarnin hana manyan tarurruka, rufe wuraren tarukan biki, da makarantu, da gidajen rawa sanadiyyar ƙara ɓarkewar annobar COVID-19.

Akwai matakan da aka ɗauka kafin gwamnatin tarayya ta yi umarnin kulle ƙasa a watan Maris, 2020.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

A wani jawabi da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Bashir Ahmad ya nuna akwai yiwuwar a sake kulle ƙasa da hana zirga-zirga.

A cewar cibiyar kula da yaɗuwar cututtuka ta Najeriya (NCDC), adadin waɗanda suka kamu da COVID-19 a faɗin ƙasar shine mutum 78,434.

Sannan kuma an sallami mutane 68,303 da suka warke daga cutar. Sai dai cutar na neman sake ɓarkewa a karo na biyu.

Korona 2.0: Hadimin Buhari ya nuna yiwuwar dawowar dokar kulle a karo na biyu
Korona 2.0: Hadimin Buhari ya nuna yiwuwar dawowar dokar kulle a karo na biyu @Thecable
Source: Twitter

A ranar 17 ga watan Disamba, 2020 an samu mutane 1,145 da suka kamu da cutar a kwana guda kacal, wanda hakan shine mafi yawa da aka taba samu a Nigeria tun bayan farkon bullar annobar.

Jihar Legas ita ce akan gaba kuma mafi muni inda ta ke da aƙalla mutane 26,700 da suka kamu da cutar.

KARANTA: Muhimman tambayoyi 6 da amsoshinsu a kan rigakafin annobar korona

Yanzu haka,Gwamnan jihar ya kamu da cutar kuma yana samun kulawa daga jami'an lafiya.

Sama da mutane miliyan 77 ne suka kamu da kwayar cutar a faɗin duniya, sannan mutane miliyan 1.7 sun rasa rayukansu sanadiyyar annobar.

Ƙasashe da dama sun sake saka dokar kulle da hana zirga-zirga don daƙile yaɗuwar cutar COVID-19.

A ranar Litinin ,Hukumomin ƙasar Saudiyya sun ɗage saukar jirage daga ƙasashen waje tsawon sati guda saboda kaucewa sake ɓullar annobar COVID-19 a kasar.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Injiniya Muneer Al-Jundi, mutumin da ya kera tare da jagorantar gina kofar dakin Ka'aba ya rasu kamar yadda sanarwa ta bayyana.

Hukumar kula da Masallatan Haramain da ke kasar Saudia ne ta sanar da mutuwar Injiniya Muneer a shafinta da ke dandalin sada zumunta.

Sanarwar ta bayyana cewa Injiniya Muneer ya rasu ne ranar Laraba a birnin Stuttgart na kasar Jamus.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel