Matashiya mai kunar bakin wake ta tada bam, ta kashe mutum 3 a Borno

Matashiya mai kunar bakin wake ta tada bam, ta kashe mutum 3 a Borno

- Wata yarinya mai karancin shekaru ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 3 da ita ta hudu a jihar Borno

- Yarinyar da ake zargin 'yar Boko Haram ce, tayi amfani da abu mai fashewa a kusa da wani masallaci da ke Kodunga

- Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, inda yarinyar tayi harin wata matattara jama'a kusa da gidan mai garin

Wata yarinya mai karancin shekaru ta yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 3 da kanta ta hudu a jihar Borno, kamar yadda majiyoyi da dama suka sanar da AFP a ranar Asabar.

"Mun kwashe gawar mutane 3 da kuma wasu mutane 2 da suka ji munanan raunuka daga wurin da lamarin ya faru," kamar yadda wani ma'aikacin taimakon gaggawa, Abubakar Mohammed ya tabbatar.

Al'amarin ya faru ne wuraren anguwar Konduga, a kalla kilomita 38 ne Maiduguri. Wacce ta kai harin ta saita abu mai fashewa kusa da inda mutane suke zama, kusa da gidan dagacin kauyen, kamar yadda wani Ibrahim Liman, shugaban 'yan sa kai ya sanar.

Matashiya mai kunar bakin wake ta tada bam, ta kashe mutum 3 a Borno
Matashiya mai kunar bakin wake ta tada bam, ta kashe mutum 3 a Borno. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku daina karyar cewa zaman aure na da wahala, Leke Adeboye

'Yan Boko Haram sun dade suna harin Konduga da sauran kauyakun da suke zagaye da shi. Wanda alamu suka nuna cewa suna harin masallatai, kasuwanni da kuma tashoshin motoci, inda suke tura mata masu kananun shekaru da abubuwa masu fashewa.

A shekarar da ta gabata, sai da suka yi sanadiyyar kashe a kalla mutane 30 a Kodunga, yayin da suka je da abu mai fashewa wurin da mutane suka taru suna kallon wasan kwallon kafa a gidan kallo.

KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matwalle na jihar Zamfara ya caccaki jam'iyyar APC a kan zarginsa da daukar nauyin ta'addanci a arewa maso yammacin kasar nan.

Idan ba a manta ba, satar daliban GSSS Kankara jihar Katsina, jam'iyyar APC ta yi zargin gwamnan PDP da kasancewa mai ruwa da tsaki a kan ta'addanci a arewa maso yamma.

Bayan jin hakan, gwamnan ya saki wata takarda, ta hannun mai bashi shawara a kan harkar labarai, Zailani Bappa, inda yace kame-kame kawai jam'iyyar take yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: