Satar yaran Kankara: Yunkuri ne na tozarta mulkina, Buhari

Satar yaran Kankara: Yunkuri ne na tozarta mulkina, Buhari

- Ceto daliban GSSS Kankara na jihar Katsina ya cigba da janyo cece-kuce a Najeriya

- Ganin yadda lamarin ya faru, shugaba Buhari ya yi zargin cewa akwai lauje a cikin nadi

- Gwamnati ta yi nazari kwarai a kan harin da aka kai wa makarantar da ke jihar Katsina

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi zargin cewa an kai wa GSSS Kankara hari ne, musamman don a tozarta shugabancinsa.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne a ranar Juma'a, 18 ga watan Disamba yayin da yake gabatar da jawabi a kan ceto yaran da aka yi a gidan gwamnatin jihar Katsina, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Buhari ya bayyana farin cikinsa a kan ganin yadda aka ceto daliban ba tare da an cutar da wani ba. Kamar yadda Buhari yace ta shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, a kan yadda satar tazo daidai da ranar da ya isa Daura, garinsa na haihuwa.

KU KARANTA: Yajin aiki: Nan babu dadewa ASUU da FG za su sasanta, Fayemi

Satar yaran Kankara: Yunkuri ne na tozarta mulkina, Buhari
Satar yaran Kankara: Yunkuri ne na tozarta mulkina, Buhari. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: An maka Buhari a gaban kotu saboda rashin sallamar shugabannin tsaro

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, mulkinsa ya yi alkawarin cewa zai dage kwarai wurin gudun kada al'amarin ya maimaita kansa.

Buhari ya yaba wa gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, a kan tabbatar da sako daliban. Ya kuma yaba wa jami'an tsaron da suka taka rawa a kan sako daliban.

Sannan Buhari ya bayyana cewa shugabannin jami'an tsaro basa yin kokarin da ya dace a kan matsalolin tsaron Najeriya.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaro ta ce rundunar Operation Hadarin Daji ta samu nasarar ceto daliban GSSS Kankara guda 344 na jihar Katsina, The Cable ta wallafa.

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara da Bello Masari, takwaransa na jihar Katsina sun ce kungiyar makiyaya shanu ra Miyetti Allah sune suka taka babbar rawa wurin ceto daliban.

Amma a wata takarda ta ranar Juma'a, kakakin hedkwatar tsaro, John Enenche, ya ce rundunar ce take da alhakin ceto yaran. A cewarsa, rundunar ta yi godiya ga jama'a musamman wadanda suka samar mu su da labaran da suka taimaka wurin ceto yaran.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng