Ku daina karyar cewa zaman aure na da wahala, Leke Adeboye

Ku daina karyar cewa zaman aure na da wahala, Leke Adeboye

- Mutane da dama suna shiga cikin fargaba saboda jin labarai a kan yadda aure yake da wahala

- Wani Leke Adeboye ya shawarci ma'aurata da su daina ce wa marasa aure, aure yana da wahala

- A cewarsa, kowa yana da halinsa, ba lallai kowa ya fuskanci wahalhalun da wani ya fuskanta ba

Fargaba tana daya daga cikin dalilan da suke hana samari da 'yan mata aure. Sau da yawa labarai za su dinga yawo a kan matsalolin aure, hakan yana sanya wa wasu su hakura da batun aure ko kuma su jinkirta yin shi.

Wani Leke Adeboye ya shawarci mutane a kan su daina tsoratar da marasa aure, ta hanyar ce musu aure yana da wahala.

Kamar yadda ya wallafa: "Ku daina ce wa mara aure, aure yana da wahala. Ba mijinki ko matarka za su aura ba."

KU KARANTA: Kankara: Iyayen dalibai sun jeru a farfajiyar makaranta suna jiran dawowar 'ya'yansu

Ku daina karyar cewa zaman aure na da wahala, Leke Adeboye
Ku daina karyar cewa zaman aure na da wahala, Leke Adeboye. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun sake damke mutumin da yayi bidiyon da ya tada zanga-zangar EndSARS

Yakamata kowa ya san cewa halayyar mutane tana da bambanci, wasu za su ji dadin aure, wasu kuma akasin hakan.

A wani labari na daban, jaridar Vanguard ta ruwaito yadda ake zargin wani mutum da daukar bidiyon wasu 'yan sanda suna kashe wani mai zanga-zangar EndSARS a cikin kasar nan, Nicholas Makolomi, wanda bidiyon ya karade ko ina a kafafen sada zumuntar zamani.

An damkesa a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba, aka zarce da shi Abuja. Kamar yadda rahoton yazo, jami'an FIB ne suka tafi dashi babban birnin tarayya.

Lauyansa, Ekenemolise Osifo, ya ce kara damkarsa a Asaba duk da babbar kotun tarayya bata amince da kama shi da rike shi tun farko ba, hakan yin karantsaye ne da doka da kuma saba wa umarnin kotu da 'yan sandan suka yi. Tuni 'yan Najeriya suka fara cece-kuce a kan kama mutumin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng