Masari karya yake, ba damu aka tattauna da yan bindigan da suka saci daliban Kankara ba: Miyetti Allah

Masari karya yake, ba damu aka tattauna da yan bindigan da suka saci daliban Kankara ba: Miyetti Allah

- Kwanaki biyu bayan samun yancin daliban Kankara, wasu sabbin bayani na fitowa

- Kungiyr Miyetti Allah ta nisanta kanta da duk wani abu dake da alaka da yan bindiga

- Gwamnati ta bayyana yadda aka samu nasarar ceto dalibai 344 daga hannun yan bindiga

Kungiyar Miyetti Allah MACBAN ta karyata cewa ta shiga cikin tattaunawa da yan bindiga wajen sakin daliban makarantar sakandare gwamnatin GGSS Kankara, a jihar Katsina.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, a ranar Laraba, ya ce gwamnatin ta tuntubi Miyetti Allah domin tattaunawa da yan bindiga kan sakin dalibai da aka sace a makarantarsu.

Sakataren kungiyar Miyetti Allah na kasa, Baba Othman Ngelzarma, ya bayyanawa Saturday Sun a hirar wayan tarho cewa bai da masaniya kan abinda Masari ke magana a kai.

A cewarsa, "sai dai idan gwamnan da shiyar kungiyarmu na Katsina yake nufi, amma ba uwar kungiya ta kasa ba."

Daga baya, Ngelzarma, ya tattauna da shugabannin Miyetti Allah na Katsina, kuma sun musanta rahoton cewa gwamnatin jihar ta tuntubesu domin shiga tsakaninsu da yan bindiga domin sakin daliban makaranta.

Hakazalika, shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Horre, Bello Abdullahi Bodejo, ya ce babu wanda ya tuntubesu ko ya tattauna da su kan lamarin.

Yace: "Bamu san yan bindigan ba kuma bamu bukatan saninsu kuma bamu da wata alaka da su. Babu wani mamban Miyetti Allah Kautal Horee ko a kauyuka da ya san yan bindigan."

KU KARANTA: Sau daya suka bamu abinci cikin kwanaki 2, inda muke barci muke bahaya: Daya daga cikin yaran Kankara

Masari karya yake, ba damu aka tattauna da yan bindigan da suka saci daliban Kankara ba: Miyetti Allah
Masari karya yake, ba damu aka tattauna da yan bindigan da suka saci daliban Kankara ba: Miyetti Allah Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yi maraba da dawowan daliban Katsina 344 (Hotuna)

Mun kawo muku cewa a ranar Alhamis, 17 ga wata aka sako daliban makarantar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 yanzu.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan.

A ranar Juma'a 11 ga wata ne 'yan bindiga suka afka GSSS Kankara da ke jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da daruruwan dalibai makarantar, bayan isar Shugaba Muhammadu Buhari Daura, garinsa na haihuwa da sa'o'i kadan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng