Shugaba Buhari ya yi maraba da dawowan daliban Katsina 344 (Hotuna)

Shugaba Buhari ya yi maraba da dawowan daliban Katsina 344 (Hotuna)

- Shugaba Buhari ya yi maganarsa ta farko bayan sakin daliban Kankara

- Shugaban kasa ya bayyana irin jaruntan Sojoji da gwamnan jihar Katsina

- Ya yiwa yara addu'an Allah ya kara kiyayesu daga wannan fitina

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi maraba da sakin daliban makarantar GGSS Kankara a jihar Katsina, mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

Buhari ya siffanta cetonsu a matsayin babban sauki ga iyayensu, kasar, da kuma duniya gaba daya.

A gajeren jawabin da ya yi bayan sanar da sakin yaran, Buhari ya mika godiyarsa ga dukkan wadanda ke da hannu wajen wannan nasara.

"Gwamna Aminu Bello Masari, da sojoji sun yi matukar kokari. Ina samun labari na tayasu murna. Sojoji sun san aikinsu. An yi musu horo kuma suna jin dadi," Buhari yace.

KU KARANTA: KARIN BAYANI: An sako daliban makarantar Kankara 344, gwamnan Katsina (Bidiyo)

Shugaba Buhari ya yi maraba da dawowan daliban Katsina 344 (Hotuna)
Shugaba Buhari ya yi maraba da dawowan daliban Katsina 344 (Hotuna) Credit: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da duminsa: Hotunan daliban Kankara 344 da aka sako da daren nan

Shugaba Buhari ya yi maraba da dawowan daliban Katsina 344 (Hotuna)
Shugaba Buhari ya yi maraba da dawowan daliban Katsina 344 (Hotuna) Credit: Femi Adesina
Asali: Facebook

Mun kawo muku cewa an sako daliban makanratar sakandaren kimiya dake Kankara akalla 340 yanzu.

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da haka.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya sanar da hakan a hirarsa na wani dan jaridan Aljazeera, Ahmed Idris.

"Kawo yanzu, an bamu dalibai 340, daga baya an kara da 4, yanzu akwai dalibai 344 dake hanyarsu ta zuwa Katsina yanzu," Masari ya bayyana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng