Yajin aiki: Nan babu dadewa ASUU da FG za su sasanta, Fayemi

Yajin aiki: Nan babu dadewa ASUU da FG za su sasanta, Fayemi

- A ranar Alhamis, gwamnan jihar Ekiti ya ce gwamnatin Najeriya tana gab da daidaitawa da ASUU

- Fayemi ya ce yana daya daga cikin wadanda suka tattauna da ASUU, kuma an kusa cimma gaci

- Ya fadi hakan ne a taron yaye daliban jami'ar jihar Ekiti wanda aka yi a cikin jami'ar da ke Ado Ekiti

A ranar Alhamis, gwamnan jihar Ekiti, kuma shugaban NGF, Dr Kayode Fayemi, ya ce kwanan nan gwamnatin tarayya za ta daidaita da ASUU, The Punch ta wallafa.

Fayemi ya ce yana daya daga cikin wadanda suka tattauna a taron daidaitawa tsakanin FG da ASUU. A matsayinsa na shugaban NGF, ya ce akwai alamar nasara. "Muna gab da daidaitawa fiye da tunanin mutane".

Gwamnan ya yi wannan maganar ne a taron yaye dalibai na 24 a jami'ar jihar Ekiti da ke Ado Ekiti, babban birnin jihar, inda fiye da dalibai 11,437 suka kammala digirinsu.

Yajin aiki: Nan babu dadewa ASUU da FG za su sasanta, Fayemi
Yajin aiki: Nan babu dadewa ASUU da FG za su sasanta, Fayemi. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: Buhari yana da kudirin alheri ga Najeriya, Bola Tinubu

Ya shawarci wadanda suka kammala karatun da su fara yin sana'o'in hannu, kada su dogara da gwamnati don su samu rufin asiri a wannan kangin da kasa take ciki.

Fayemi ya ce, "Kowa ya yarda da cewa malamai da dalibai masu ingantaccen ilimi suna da damar samar da cigaba a kowacce kasa. Don haka ina mai tabbatar wa da wadanda suka kammala karatu cewa su jari ne. Gara su fara sanin cewa su manyan mutane ne, don su ciyar da kasar nan gaba."

KU KARANTA: Budurwa mai shekaru 24 ta aura jakar da ta yi soyayya da ita na shekaru 5

A taron, sarkin Kano na 14, Muhammadu Sunusi II, shugaban jami'ar ya ce, "Ba ni wannan damar za ta bani damar hada karfi da karfe da Fayemi, don mu yi iyakar kokarinmu na kawo karshen matsalolin da Najeriya take fuskanta".

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari ya ce ana tattaunawa da 'yan bindigan da suka sace daliban GSSS Kankara ta Kungiyar masu kiwon shanu ta Miyetti Allah ta Najeriya, MACBAN.

A kalla 17 daga cikin daliban sun tsere daga wurin masu garkuwa da mutanen, kuma sun koma wurin iyayensu. Ya musanta batun mutuwar wani daga cikin daliban.

Sannan jami'an tsaro da wasu majiyoyi sun sanar da AFP cewa Boko Haram ne suka horar da wasu 'yan bindiga don su sace daruruwan daliban GSSS Kankara, jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel