Takarar Atiku a 2023: Uwar jam'iyyar PDP ta yi fashin baki

Takarar Atiku a 2023: Uwar jam'iyyar PDP ta yi fashin baki

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, zai iya takaran kujeran shugaban kasa karkashin PDP a 2023

-Shugaban uwar jam'iyyar, Uche Secondus, ya sanar da hakan bayan ganawar sirri da jigogin jam'iyyar a Bauchi

- Secondus ya ce ba'a maye gurbin Atiku da kowa ba amma jam'iyyar zata zabi dan takara a demokradiyyance

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata zargin cewa tayi watsi da dan takaranta a zaben shugaban kasan 2019, Atiku Abubakar, domin zaben wani a 2023.

Daily Sun ta ruwaito cewa shugaban uwar jam'iyyar, Uche Secondus, ya karyata labarin bayan ganawarsa da wasu gwamnonin jam'iyyar a Bauchi.

Secondus ya ce jam'iyyar za ta tabbatar da cewa duk wanda ya cancanci takara zai iya ba tare da tsangwama ba.

Yace: "Wannan jam'iyyar tana abubuwanta a demokradiyyance ne. Babu nuna wariya. Duk wanda ya cancanta, tsoho ko yaro, gwamna ko tsohon gwamna, zai samu daman takara."

Wadanda suka halarci zaman sune mataimakin shugaban jam'iyyar na Arewa, Sanata Nazif Suleiman Gamawa, da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark.

Hakazalika akwai gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Gombe, Hassan Ibrahim Dankwambo.

Gwamnan jihar Bauchi, AbdulKadir Bala, ne ya karbi bakuncinsu.

KU KARANTA: Ba zamu koma aji ba sai an biya mana bukatunmu - Kungiyar ASUU ta yi tsokaci kan bude makarantu

Takarar Atiku a 2023: Uwar jam'iyyar PDP ta yi fashin baki
Credit: @atiku
Asali: Facebook

KU DUBA: Sabbin mutane 126 sun kamu da Korona, yayinda ake gab da isa 60,000\

A bangare guda, Jiga-jigan Jam'iyyun APC Da PDP sun ajiye siyarsu gefe guda yayinda suka halarci daurin auren 'dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar Da 'Yar tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa, Nuhu Ribadu.

An daura auren Aliyu Atiku Abubakar ne da Fatima Nuhu Ribadu a yau Asabar a Aso Drive dake Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel