Da duminsa: Gwamnan Legas ya bada umurnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandaren jihar
Gwamnatin jihar Legas ta bukaci a rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu nan da ranar Juma'a.
Hakan na kunshe cikin jawabin da aka saki ranar Alhamis mai take 'LASG na umurtan dukkan makarantu suyi hutu ranar Juma'a, 18 ga Disamba, 2020'
A jawabin, dirakta janar na ofishin lura da ingancin makarantu na ma'aikatar ilimi, Mrs Abiola Sereiki-Ayemi, tace, "a kawo karshen zangon farko na shekarar 2020/2021 a dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu ranar Juma'a, 18 ga Disamba, 2020."
"Gwamnatin jihar Legas na umurtan dukkan makarantu su bada hutu ranar Juma'a."
"Saboda haka, dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu dake kasa da jami'a su kulle makarantu don hutun Kirismeti da sabon shekara."
"Makarantu zasu dawo ranar Litinin, 4 ga watan Junairu, 2021 bisa jadawalin bai daya na jihar Legas."
KU KARANTA: Rashin tsaro da Korona: Jihohin Arewa 5 da suka rufe makarantunsu
KU DUBA: Harin Kankara: Gwamna Masari ya kulle dukkan makarantun kwana a jihar Katsina
Kun ji cewa daliban kwalejin Ilimin Sa’adatu Rimi dake jihar Kano sun fito gudanar da zanga-zangan nuna rashin amincewa da umurnin rufe makarantu gaba da sakandare da gwamnatin jihar tayi.
Rahoto daga gidan rediyon Arewa 93.1 na nuna cewa daliban makarantar dake karamar hukumar Kumbotso sun tare hanyar titin Kano zuwa Zaria.
Hakan ya kawo tsaiko ga matafiya dake bin hanyar yanzu haka.
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ta bada umurnin rufe jami'ar Bayero da sauran makarantun gaba da sakandaren dake jihar ba tare da bata lokaci ba.
Wannan sanarwan ya zo kwana daya bayan gwamnatin jihar ta kulle dukkan makarantun firamare da sakandaren dake jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng