Bayan kashe N28bn kan Korona, ministan Abuja ya ce ta dawo kuma ta fi hadari yanzu

Bayan kashe N28bn kan Korona, ministan Abuja ya ce ta dawo kuma ta fi hadari yanzu

- Ministan birnin tarayya yayi kukan yadda mutan Abuja ke dawo da cutar Korona

- Mallam Musa Bello ya ce za'a sake sanya dokar kulle a fadin Abuja

- Ya yi kira ga shugabanni su sanya baki domin kawo karshen wannan annobar

Ministan birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Belli, ya yi shellar dawowar cutar Korona cikin Abuja kuma ta fi na baya hadari wajen kwasan mutane.

Ya ce hukumar birnin tarayya na iya sanya dokar kulle idan mazauna birnin basu daina saba dokokin da aka gindaya ba.

Belli, ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki kan dawowar annobar Korona.

Ya ce rashin biyayyan mutane kan ka'idojin da hukumar NCDC ta gindaya ya haifar da dawowar cutar.

Ya tabbatar da cewa lallai za a sake sanya dokar hana fita.

"Saboda wannan shine hanya daya tilo wajen kare rayukan mutane. Wajibi ne mu sani cewa COVID-19 ta dawo kuma ta dawo da karfi," yace.

"Ta na kashe mutane kuma wajibi ne dukkan shugabanni na addini na gargajiya da gwamnati su koma unguwanninsu su bayyanawa mutane."

"Mun san an gaji; kowa ya gaji da COVID-19 amma gaskiyar maganar itace ta dawo."

A ranar Litinin, mutane 86 suka kamu da cutar Korona a birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa kakakin majalisar dokokin jihar Kano yayi murabus

Bayan kashe N28bn kan Korona, ministan Abuja ya ce ta dawo kuma ta fi hadari yanzu
Bayan kashe N28bn kan Korona, ministan Abuja ya ce ta dawo kuma ta fi hadari yanzu Credit: @NCDCgov
Source: Twitter

KU DUBA: COVID-19: Gwamnatin Kaduna ta sanar da rufe dukkan makarantun jihar a karo na 2

A bangare guda, ministan birnin tarayya Abuja, Muhammadu Musa Bello, ya bayyanawa majalisar dattawan tarayya cewa ya kashe kimanin bilyan 29 domin dakile cutar Korona a Abuja.

Yayin jawabi ga mambobin kwamitin birnin tarayya na majalisar dattawa, Ministan yace an kashe kudaden ne wajen inganta tsaro, kayan abincin rage radadin Korona, da kuma jihohin dake makwabtaka mabukata.

Ya kara da cewa gwamnatin Abuja ta taimakawa mazauna birnin da makwabta da kayayyakin kiwon lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel