Lockdown gadan-gadan: Korona ta harbi sabbin mutane 930 a Nigeria

Lockdown gadan-gadan: Korona ta harbi sabbin mutane 930 a Nigeria

- Alamu na nuni da cewa da gaske annobar korona ta sake yunkurowa a karo na biyu

- Alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar sai kara hawan gwauron zabi suke yi a 'yan kwanakin baya bayan nan

- Jihohi sun fara bayar da umarnin rufe makarantu, musamman ma Firamare da Sakandire

Alkaluman baya bayan nan akan mutanen da annobar cutar korona ke kamawa a Nigeria suna saka damuwa a zukatan jama'a tare da fargabar cewa za'a koma gidan jiya.

Mutane 930 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Laraba, 16 ga watan Disamba, kamar yadda ya ke a sakon sanar da alkaluman sabbin mutane da cutar ke kamawa wanda NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 75,062 a Najeriya.

Daga cikin mutane sama da 70,000 da suka kamu, an sallami 66,775 yayinda 1190 suka rigamu gidan gaskiya.

KU KARANTA: Abubuwa 15 da ya kamata ka sani game da Buhari yayinda ya cika shekaru 78 yau

Lockdown gadan-gadan: Korona ta harbi sabbin mutane 900 a Nigeria
Lockdown gadan-gadan: Korona ta harbi sabbin mutane 900 a Nigeria Credit: @NCDCgov
Asali: Twitter

Ga jerin adadin wadanda suka kamu a jihohin Najeriya:

Lagos-279

FCT-179

Plateau-62

Kaduna-54

Kano-52

Katsina-52

Imo-42

Jigawa-42

Rivers-38

Kwara-30

Nasarawa-19

Yobe-15

Ogun-13

Borno-10

Oyo-9

Niger-9

Ebonyi-6

Bauchi-6

Edo-5

Taraba-4

Sokoto-2

Cross River-2

KU KARANTA: Shugaban kasan Faransa, Emmanuel Macron ya kamu da cutar Korona

A bangare guda, ministan birnin tarayya, Malam Muhammad Musa Bello, ya yi shellar dawowar cutar Korona cikin Abuja kuma ta fi na baya hadari wajen kwasan mutane.

Ya ce hukumar birnin tarayya na iya sanya dokar kulle idan mazauna birnin basu daina saba dokokin da aka gindaya ba.

Bello, ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki kan dawowar annobar Korona. Ya ce rashin biyayyan mutane kan ka'idojin da hukumar NCDC ta gindaya ya haifar da dawowar cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel